D’Tigress ta shiga jerin ƙwararrun ƙungiyoyin ƙwallon kwando 10 na duniya

Spread the love

Hukumar ƙwallon Kwando ta Duniya (FIBA) ta bayyana cewa, ƙungiyar ƙwallon ƙwando ta Mata ta Nijeriya, D’Tigress, ta hau matsayi na takwas a jerin ƙasashe na duniya bayan rawar da ta taka a Gasar wasannin Olympics na 2024 a Paris.

A ranar Alhamis FIBA ta fitar da jerin sunayen ƙasashen.

Wannan ƙarin matsayi ya tabbatar da matsayinsu a cikin manyan ƙungiyoyi goma na duniya, wanda ya sa suka zama ƙungiyar Afirka ta farko, maza ko mata, da ta kai wannan matsayi a jerin ƙasashe na duniya na FIBA.

ƙungiyar ta D’Tigress, it ace ta farko a nahiyar Afirka da ta taɓa kai wa zagayen wasan kusa da na ƙarshe a wasannin na Olympics.

By ukarofi