Daga AISHA ASAS
Shahararriyar mawaƙiyar Amurka, Mariah Carey, ta sanar da rasuwar mahaifiyarta, Patricia, da ‘yar uwarta, Alison, waɗanda suka rasu a rana guda.
A cikin wani saƙo mai ratsa jiki da ta rabawa manema labarai a ranar Litinin, mawaƙiyar ta bayyana matuƙar baƙin cikinta game da rasuwar ‘yar uwanta mutuwar fuju’a.
“Zuciyata cike da baƙin cikin rashin mahaifiyata a ƙarshen makon da ya gabata. Abin ƙarin baƙin ciki, a cikin wannan mummunan yanayi, ‘yar’uwata ta rasa ranta a wannan rana,” Carey ta bayyana.
Mawaƙiyar da ta lashe kyautar Grammy ta nuna godiya ga lokaci mai daraja da ta yi tare da mahaifiyarta kwanan nan. Ta ƙara da cewa “Na albarkantu da damar kasancewa da mahaifiyata a makon da ya gabata wanda ya kasance makonta na ƙarshe a duniya. Ina godiya da ƙauna da ƙwarin gwiwa da ku ke ba ni, kuma ina mai neman mutane su mutunta sirrina a wannan mawuyacin lokacin da nake ciki,” inji ta.
Ba a bayyana musabbabin mutuwar Patricia mai shekaru 87 da Alison mai shekaru 63 ba. Duk da haka, babban abokin Alison kuma mai kula da ita, Daɓe Baker, ya bayyana wa jaridar The U.S. Sun cewa Alison ta kasance tana samun kulawar asibiti a cikin makonnin da suka gabata, sakamakon fama da matsalolin lafiya, gami da matsalolin wasu sassan jiki.
“Alison mutum ce mai hazaƙa, mai daɗin zama, kuma mai hankali,” inji Baker.
Ya ƙara dacewa, “Na san ta tsawon shekaru tara a matsayin abokinta, kuma a cikin ‘yan watannin nan, mai kula da ita, zan yi kewarta sosai. Fatan alheri, Alison. Da fatan za ki samu kwanciyar hankali, ruhinki ya tsarkaka daga kowane irin azaba, da aka azabtar da ke daga azabar duniya.”
Dangantakar Mariah Carey da mahaifiyarta, Patricia, sananniya ce wadda ke cike da sarkakiya. Patricia, tsohuwar mawaƙiyar opera da aka horar a Juilliard a birnin New York, ta kuma yi aiki a matsayin mai koyar da murya, kuma a baya ta auri Alfred Roy Carey, wanda ya rasu a shekara ta 2002. Ma’auratan sun rabu tun a lokacin da Mariah ke da shekaru uku a duniya.
“Kamar abubuwa da yawa na rayuwata, tafiyata tare da mahaifiyata na cike da saɓani da zahiri,” Mariah ta rubuta.
Ta ƙara da “Ba wai kawai baƙi da fari za a iya fassara dangantakarmu ba, ya kasance bakan gizo. Dangantakarmu igiya ce mai tsauri ta girman kai, zafi, abin kunya, godiya, kishi, sha’awa, da rashin jin daɗi. ƙauna ce mai sarƙaƙƙiyar ma’ana. Kawalwalniyar soyayya ce sarƙe a zuciyata ga mahaifiyata,” Mariah Carey ta faɗa a cikin tarihinta na 2020, dangane da alaƙanta da mahaifiyarta.

