Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Daga jin taken rubutuna na wannan makon na san abin da zai fito a bakin wasu shi ne, ai faɗa ma ɓata baki ne! Talaka kam ya daɗe da shiga cikin tasku ba tun yanzu ba. Babu wani lokaci da talakawa ke ji a jikinsu a tarihin ƙasar nan kamar wannan lokaci da rayuwa ke ƙara tsada, abubuwa suke cigaba da canjawa ba zato ba tsammani. Farashin kayan masarufi na daɗa tashin gwauron zabi, a wasu wurare ma ya ninka kuɗinsa na baya. Naira dubu biyar ta zama wa talaka kamar Naira ɗari biyar. Mutum ba ya iya cefane da ita, ya kai gida da ƙwarin gwiwa, sai dai ya shiga da ’yar ƙaramar leda jiki a sanyaye, fuska ba fara’a!
A ’yan shekarun da na yi a duniya, ina iya tunawa tun da gwamnatin mulkin soja ta tsohon shugaban ƙasa Ibrahim Badamasi Babangida ta ɓullo da tsarin sauya fasalin tattalin arziki, da ta kira da Structural Adjustment Programme, wato SAP a taƙaice, har yau tunanin talakan ƙasar nan bai dawo daidai ba. Abubuwan da mutum ke ganin damar su sun zo sun fi ƙarfinsa. Farashin man fetur kullum sai gaba-gaba yake yi. Kuma kowacce gwamnati ta shigo tana zuwa ne da alƙawarin daidaita al’amura, amma ita ma da ta hau, sai ka kasa gane ina ta dosa. A maimakon a toshe ƙofofin da ake samun damuwa, sai ka ga kullum damuwoyin ƙara yawa suke yi. Kowacce gwamnati na ɓullo da nata tsare-tsaren tattalin arzikin da nufin bunƙasa hanyoyin samun kuɗaɗe, amma kuma a ƙarshe matsala hakan ke haifarwa ga rayuwar talaka.
Dubi dai yadda jama’a suka riƙa kokawa da salon mulkin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, saboda tsare tsaren inganta tattalin arziki da ya riƙa ɓullo da su waɗanda suka riƙa jefa talaka cikin ƙunci. Yanzu da sabuwar gwamnati ta shigo wacce ake kyautatawa tsammanin za ta zo da sauye-sauye da za su faranta ran talaka, sai ga shi ita ma tun ba a je ko’ina ba ta fara shigo da wasu sauye-sauyen da ke ƙara tsananta halin da ake ciki a maimakon a samu sassauci.
Cikin ƙasa da watanni biyu, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ƙara farashin man fetur, wanda shi ne ƙashin bayan rayuwar talakan ƙasar nan, domin kuwa farashin komai na ƙasar nan yana juyawa ne bisa ga farashin litar man fetur. Komai ƙanƙantar abin da za ka saya, sai an auna shi da farashin litar mai, don a cire masa farashin da zai yi daidai da shi a kasuwa, zuwa ga kantin da ka ke sayayya.
A dalilin haka, komai ya canja farashi, har abin da a baya ba a ɗauke shi a bakin komai ba, kamar gishirin miya, farashinsa ya canza. Rayuwar zamantakewar iyali ta shiga wani hali, ala dole mata sun rage ɗagawa mazaje hankali saboda ba a samu yadda suke so ba, sakamakon yadda suka ga zahirin yadda rayuwa ta juyawa mazajensu baya. A wuraren da ake bar wa mata kuɗin cefane a hannunsu, sun ga yadda kasuwa ta gagari talaka. Rayuwa ta koma kan zancen abin da za a ci a gida, ba me za a samu na jin daɗin rayuwa ba. Masu ababen hawa, sun fara gagara fita da motocinsu ko babura, saboda rashin kuɗin sayen mai, ballantana masu janareto wasu tuni sun jingine nasu a gefe, an zubawa sarautar Allah ido.
Ba talaka kaɗai ba, hatta masu ɗan dama-dama su ma sun fara kasawa, saboda nauyin iyali da na ‘yan uwa da ya dawo kansu ya sa su ma kokawa da rayuwar. Mutumin da a da yake kyautar dubu biyar zuwa goma ba tare da ya ji komai ba, yanzu ba ya iya ba ka dubu biyu ko dubu ɗaya. Sai an yi sa’ar gaske kafin a samu wanda zai rufe ido ya tausaya, har ya taimaka maka da wani abu, ko da kuwa kuɗin motar da zai mayar da kai gida ne.
A Nijeriya ta yau, da talaka da mai kuɗi duk an shiga wani hali, sai dai kawai a ce wani ya fi wani dama-dama ko ɗan sassauci. Babu ma abin tausayi irin ƙaramin ma’aikacin gwamnati, wanda albashinsa dama da ƙyar yake yi masa mako ɗaya. Al’umma na yi masa kallon mai gata, saboda kowanne wata yana karɓar albashi, amma kuma rayuwarsa ko ta iyalinsa ta zama abin Allah sarki. Shi ne sarkin cin bashi a unguwa ko roƙon cikon kuɗin motar zuwa wajen aiki. Shekara da shekaru an kasa daidaita albashin ma’aikata, alhalin ba a gaza ƙara farashin man fetur da sauran kayan masarufi a kasuwanni.
Turancin masana tattalin arziki da manazarta ya kusa ƙarewa a kan bincike da bayanin halin da ƙasar nan take ciki. Babu wani rubutu da ba a yi ba, babu wata shawara da ba a bayar ba. ƙwararru kan tattalin arziki, manyan masana, da irin mu ’yan kuci-ku-bamu, masu sharhi a jaridu da gidajen rediyo, ana ta bayanai da tayar da jijiyar wuya game da yanayin da ake ciki, amma kamar ana rubutu ne a kan ruwa. Gwamnati da muƙarrabanta suna nasu turancin daban, ’yan boko da kwamarori na ta kumfar baki a gefe.
A yayin da gwamnati ke cewa za ta raba tallafin da zai ragewa talaka raɗaɗin ƙuncin da yake ciki, a sakamakon janye tallafin man fetur da ta yi. ƙungiyoyin ƙwadago na kira da a maimakon haka a ƙara albashin ma’aikata, da rage haraji da sasauta wasu tsare-tsaren gwamnati, don tsananin da ake ciki ya yi sauƙi. Masu nazarin tattalin arziki na ganin dole ne sai an zabtare albashin manyan masu riƙe da muƙaman gwamnati, a buɗe iyakokin ƙasa, don shigo da kaya daga ƙasashen waje, domin farashin na gida ya sauka. Gwamnati da jami’anta su rage yawan kuɗaɗen da suke kashewa wajen tafiyar da harkokin gwamnati da na ƙashin kansu ta yadda za a yi amfani da rarar da aka samu wajen sassauta rayuwar talaka, a maimakon na sama su riƙa jin daɗi su kaɗai da iyalansu.
Ba lallai ne gwamnati ta nace kan sai ta hanyar ƙara farashin ne kaɗai za a iya farfaɗo da darajar Naira ba. ƙoƙarin shugaba Bola Ahmed Tinubu na kawo sauyi kan kasuwar hada-hadar kuɗaɗe wanda ya ci karo da tashin farashin dala, da aka rawaito cewa, dala ɗaya ta kai naira ɗari takwas a kasuwar canji, a maimakon Naira ɗari biyar da wani abu, babban abin ɗaga hankali ne. Amma hakan na nufin idan ba ƙara farashin mai aka yi ba, babu wata hanya da ƙwararru da mahukunta a ƙasar nan za su gano ta samar da kuɗaɗen shiga, don ɗaga darajar Naira, sai dole an ɗauki matakan da za su ƙuntatawa talaka? Wacce riba ake so a cimma, idan har wanda aka ce ana yi ne domin sa, ba ya gani a ƙasa, sai dai tsabar jin jiki da shiga halin ni-’ya-su?
Matuaar shugaban ƙasa Tinubu ba ya son ya ɓata rawarsa da tsalle, lallai ne ya ɓullo da sabbin tsare-tsaren da ba za su tsanantawa talaka ba, maimakon haka ma za su ƙara sauƙaƙa masa rayuwa ne, ya samu sassauci da walwala a rayuwarsa. Ita ma kuma gwamnati a gefe guda ta samu canjin da take so ta samu. Gaskiya an kusa kai talaka bango, kada a riƙa ɗaukar haƙurin sa da juriyarsa a banza. Ba ma fatan ganin irin abubuwan da suke faruwa a wasu ƙasashe na zanga-zanga da ƙone-ƙone, sakamakon tsadar rayuwa suna faruwa a ƙasar nan. Don haka dole ne shugabanni su tashi tsaye su gano wasu hanyoyi na samar da sassauci.
Rabon kuɗi ga talakawa da sunan tallafi ba shi ne mafita ba, don haka ne ma wasu masana da ƙungiyoyin ma’aikata ke kuka a kai. Saboda a baya mun ga yadda gwamnoni da ’yan siyasa suka handame tallafin abinci da aka ce gwamnati ta bayar a rabawa talakawa da sunan tallafin Korona. Da ƙyar wasu suka samu sunƙin taliya ɗaya, wasu ma babu, ga kokawa da fashe-fashen dukiyar gwamnati. Wannan shirin ma da gwamnati ke yi na rabon tallafin kuɗaɗe ba lallai ya kai ga talakawan da ake nufin ya kai garesu. ’Yan siyasa ne za su wawushe da sunan kason mutanen su, ’Yan jam’iyya, ko waɗanda suka taya su yaƙin neman zaɓe, ba ainihin talakawa irina da irinki ba.
