Yadda mahaifiyar Yar’Adua ta mayar da ni abin da na zama a yau – Jonathan

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana takaicinsa game da rasuwar Hajiya Dada Yar’Adua, Mahaifiyar Tsohon shugaban ƙasa, Umaru Musa Yar’Adua inda ya ce ta yi tasiri sosai ga nasarorin da ya samu a rayuwarsa.

Jonathan ya faɗi haka ne a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyyar rasuwar Hajiyar ga iyalanta a Katsina, a ranar Asabar da ta gabata.

Ya ce, “mutuwarta ta matuƙar sosa mun rai. Ɗanta ne ya ɗakko ni a matsayin abokin tafiyarsa wanda ba don ita ba, da yau ba ku san sunana ba.”

Tsohon shugaban ƙasar ya bayyana cewa, ta kasance kamar mahaifiya a gare shi kuma kamar mutuwar mahaifiyarsa ce, ya na mai cewa ya ji labarin mutuwarta ne a lokacin da ya ke kan hanyar zuwa Kigali a ƙasar Ruwanda inda bayan ya dawo ne a ranar Juma’a, sai ya garzaya Katsina don jajentawa ga rasuwartata.

Ya kuma ce, a madadin sa da jama’arsa da ma ƴan jiharsa, su na miƙa gaisuwar ta’aziyya ga iyalan Yar’Adua da al’ummar jihar Katsina baki ɗaya.

Daga ƙarshe, ya yaba wa marigayiyar wacce ya ce ta kasance mai kirki da albarka kuma wacce ta haifo ƴaƴan da suka bada gudunmawa sosai wajen samar da ci gaba a Nijeriya.

By Babaji