Ina maka fatan alkhairi kan ajiye aikinka – Shugaba Tinubu ga Ngelale

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ofishin shugaban ƙasa ya ce ya samu saƙo daga mai magana da yawun Shugaba Bola Tinubu, Ajuri Ngelale cewa zai ajiye aikinsa saboda dalilai na kai-da-kai da kuma matsala ta kiwon lafiya.

An samu sanarwar ne ta shafin ofishin na X inda ta ce an karɓi uzurin Ngelale na tafiya hutu daga aikinsa.

“Shugaban ƙasa ya amince da dalilansa na tafiya hutu, ya fahimce su kuma ya tausaya game da matsin da suka kai ga yanke wannan hukunci mai tsauri”, inji sanarwar.

Ofishin, ya kuma yaba wa ƙoƙarinsa na sadaukarwa wajen hidimta wa ƙasa da kuma miƙa godiya a gare shi na gudunmawar da ya bayar a matakai daban-daban musamman a harkokin da suka shafi ƙasa.

Ofishin ya kuma yi kira ga al’umma, su girmama sirrin Ngelale da iyalansa kamar yadda ya buƙaci a ɓoye su yayin ajiye aikin nasa.

A baya dai, Ngelale ya sanar da yanke ajiye aikinsa na ɓangaren harkokin ofishin shugaban ƙasa, inda ya ce zai yi haka ne saboda matsaloli na cikin gida.

By Babaji