Ainihin dalilan da suka sanya Ngelale yin murabus daga muƙamin kakakin Tinubu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wasu sabbin bayanai sun bayyana game da dalilan da suka sanya mai taimaka wa shugaba Tinubu na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya yi murabus daga aikinsa.

A ranar Asabar ne Ngelale ya sanar cewa, ya ɗauki hutu mara iyaka don matsalolin kiwon lafiya da ya shafi ahalinsa.

Ya bayyana haka ne kwana ɗaya bayan miƙa wata takarda ga ofishin shugaban ma’aikata na Fadar shugaban ƙasa kan cewa ya sanar da shugaban ƙasa batun ajiye aikin nasa.

Bayan fakewa da matsalolin kiwon lafiya a matsayin dalilinsa na tafiya hutu mara iyaka, wata majiya ta bayyana wa jaridar ‘DAILY NIGERIAN’ cewa, zaɓi aka bai wa Ngelale ya sauka daga muƙamin Kakakin shugaban ƙasa, wanda hakan ya sa ya sauka daga dukkan ɓangarorin da aka naɗa shi.

Tun lokacin da aka ba shi muƙamin Kakakin, wanda iyalansa sun yi tasiri wajen naɗa shi, an yi ta samun matsi kan a maye gurbinsa da wani wanda shugaban ƙasa ya fi amincewa da shi.

Sannan, an gano cewa cikin jami’an labarai da Tinubu ke aiki da su, ana zargin cewa Ngelale ya yi musu fintinkau wajen gudanar da harkokin ofishin.

Wata majiya ta bayyana cewa, Ngelale ya mamaye ayyuka da dama sama da asalin abin da ya ke nauyinsa ne.

Majiyar ta kuma ce, kasancewar Ngelale shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan kwamitin jakadancin kula da yanayi da ayyukan raya ƙasa, ya taimaka wajen sanya manyan jami’an gwamnati su nemi Tinubu ya maye gurbinsa da wani inda aka ba shi zaɓi kan wane muƙami zai ɗauka cikin biyun.

Ganin haka ne ya sa Ajuri ya zaɓi cigaba da kasancewa kakakin madadin shugaban kwamitin wanda shi aka yi tunanin zai zaɓa.

Rashin amincewa da Ngelale ya yi da hukuncin da manyan jami’an suka yi, ya sanya suka umarce shi ya ajiye aikin kakakin.

Sakamakon haka ne ya sa Ngelale ya ajiye baki ɗaya muƙaman da aka ba shi, kamar yadda majiya mai ƙarfi ta bayyana.

By Babaji