Gwamnan Zamfara ya ƙaddamar da aikin babban asibiti mai ɗaukar gadoji 200 a Talata Mafara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada aniyar gwamnatinsa na zuba ayyuka a harkokin kiwon lafiya a jihar ganin yadda manyan asibitoci ke taka rawar gani a ɓangaren.

A ranar Asabar ne gwamanan ya ƙaddamar da sake ginawa da kuma zuba kayan aiki na babban asibiti a ƙaramar hukumar Talata Mafara wanda zai ɗauki aƙalla gadojin marasa lafiya 200.

Wata takarda da Kakakin gwamanan, Sulaiman Bala Idris ya fitar ta ce, tsohon gwamnan tsohuwar Jihar Sakkwato, Malam Yahaya Abdulkarim shi ne babban baƙo na musamman a taron.

A lokacin da ya ke jawabi, gwamana Lawal ya nuna damuwa kan yadda aka watsar da batun asibitin ƙaramar hukumar wanda ya rasa kayayyakin aiki da kuma rashin kulawa na tsawon shekaru inda hakan ya sa shi ganin dacewar su waiwayi ɓangaren kiwon lafiya da gwamnatocin baya suka yi buris da shi.

Ya ce, da yardar Allah zai cika alƙawarin da ya ɗauka wattani kaɗan da suka gabata a lokacin da ya kai ziyara asibitin da kuma jami’ar jihar, ta yadda aikin asibitin zai kammala don bunƙasa garin Talata Mafara a matsayinsa na wajen gudanar da harakokin kasuwanci.

Ya kara da cewa, kasancewar za su sanya kayayyakin aiki na zamani, asibitin zai zama waje da al’umma za su ke karɓar kulawa cikin ƙanƙanin lokaci.

Ana sa ran za a kammala aikin cikin watanni shida masu zuwa.

Daga ƙarshe, Tsohon gwamnan Sakkwato, Malam Yahaya Abdulkarim, ya yaba wa gwamnan kan sanya ɓangaren kiwon lafiya a matsayin ɗaya daga cikin muhimman ayyukan gwamnatinsa.

By Babaji