Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Kamfanin Matatar man fetur ta Ɗangote, ya sanar da cewa da zarar ya kammala wasu muhimman abubuwa da kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPC), man fetur ɗin kamfanin zai shiga kasuwa.
Shugaban kamfanin, Aliko Ɗangote ne ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a ranar Talata, biyo bayan ƙaddamar da kason farko na man daga matatar kamfanin mai ganga 650,000 a kowace rana.
Dangote ya tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa za su iya sa ran samun man fetur mai inganci da daɗewa
“Ba za ku ƙara fuskantar matsalolin da injinan motoci ke baku ba,” inji Ɗangote.
“Man fetur ɗin mu zai yi daidai da na kowace ƙasa a duniya; babu wanda zai wuce mu ta fuskar inganci,” inji shi.
Dangote ya jaddada fa’idar tattalin arzikin da ayyukan matatar kamfanin ke da su, inda ya bayyana cewa za ta taimaka wajen farfaɗo da masana’antu a Nijeriya tare da daidaita darajar naira da kuma taimakawa wajen rage hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa,” inji shi.
Matatar mai ta Dangote da ke Legas ta dala biliyan 20, ta fara aiki a watan Disambar da ya gabata.
