Diloli ne silar tsadar siminti a Nijeriya – BUA

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban Kamfanin Siminti na BUA, Alhaji Abdul Samad Rabi’u, ya bayyana yadda ’yan kasuwa, musamman diloin siminti suka yi watsi da manufar kamfaninsa na sayar da siminti a kan N3,500 kan kowacce buhu a shekarar da ta gabata, inda ya ce zarge su da zama silar tsadar da siminti ya yi a faɗin Nijeriya.

Shugaban kamfanin ya bayyana hakan ne a babban taron kamfanin karo na takwas a Abuja, ranar Alhamis.

AbdulSamad ya ce, dillalan ne ke kawo cikas ga dukkanin wani shirinsa na sauke farashin siminti.

AbdulSamad ya bayyana cewa kamfanin simintin BUA ya sanya farashin buhun siminti mai nauyin 50kg a kan N3,500, matakin da zai sauƙaƙa simintin ga masu amfani da shi.

Sai dai shugaban kamfanin na BUA ya ce wannan rage farashin bai kai ga mutane gama gari ba da ‘yan kasuwar suka ƙi sauke farashinsu.

Da yake ƙarin haske a wurin taron, BUA ya ce kamfaninsa ya sayar da sama da tan miliyan ɗaya na siminti ga dillalan a ƙasa da N3,500 kan kowane buhu.

“Mun sayar da siminti ga dillalai kan farashin da za su iya sayar da shi kan N3,500 amma burinsu na samun riba mai yawa ya sa suka rika sayar da shi sama da N7,000.”

AbdulSamad ya yi takaici, yana mai nuni da cewa son zuciya na waɗannan dillalai da faɗuwar darajar Naira ne suka jawo tashin farashin da ake gani a kasuwa. 

Duk da wannan ƙalubalen, Rabiu ya jaddada cewa siminti na BUA ta himmatu wajen ganin an samu raguwar farashin duk da faɗuwar darajar Naira. “Siminti a yau yana da rahusa sosai idan aka kwatanta da bara lokacin da aka daidaita don canjin canjin kuɗi,” inji shi.

Duk da wannan cikas, kamfanin BUA Cement ya bayar da rahoton samun ribar da aka samu bayan harajin da ya kai biliyan N69.5 tare da bayyana ribar N2 a kowace kaso.

By ukarofi