Tafiyar Matasa 2027

Spread the love

UNCLE LARABI

Ya kamata tun yanzu matasa su ɗaura babbar ɗamara akan wannan tafiyar. Gaskigar magana tsofaffi ba zasu iya riƘe Ƙasar nan ba. Lissafi ya nuna tsoffi biyu sune suka kashe Ƙasar nan. Yayin da a baya tarihi ya nuna cewar Ƙasar ta rayu ta yi albarka ne a hannun matasa irin na jiya. Tun daga kan Tafawa Balewa da Nnamdi Ezekwue da su Yakubu Gawon da Murtala Ramat da Obasanjo a mulkinsa na farko (1979). Da su Shehu Shagari da Buhari matashi na (1984) da Babangida da Shonikan da Abacha da Abdulsalamu Abubakar da Obasanjo mulkinsa na biyu (1999) da Marigayi Umar Yar’adua da Jonathan babu wanda ya haura Shekaru 55 Sanda ya mulki Nijeriya. A cikinsu ma akwai wanda ya ke Shekaru 20 da wani abu.

Mafi yawan cin su yan Shekaru 28 zuwa 32 ne. Wasu ne a cikinsu Ƙalilan suka mulki Nijeriya suna yan Shekaru 40 da wani abu zuwa 55. Amma tunda muka miƘa mulki ga tsoffin nan guda biyu ‘yan sittuna wa saba’una shikenan Nijeriya lissafinta ya Ƙwace. Wasu na ganin matasan yanzu nagartarsu bata kai ta matasan da wancan lokacin ba. Don haka in an barsu da mulkin Ƙasar ma za’a sake shiga wani mawuyacin halin ne fiye da wanda tsoffin su ka jefa Ƙasar.

Gaskiya ba haka bane. Akwai matasa masu nagarta da gaskiya da amana fiye ma da matasan waɗancan zamanin kawai dai dacen samun su ne sai an tona. Amma gaskiyar magana idan aka cigaba da wannan tafiyar ta tsohon da ya takwarkwashe ya tsohuwar bukka ace shi zaizo ya mulke mu to akwai Ƙura da zata cigaba da bude dukkan ‘yan Ƙasar nan. Don waɗannan tsoffin babu abinda zasu iya yiwa kasar Illa kwakyara da kashe mu raba tunda ƘwaƘwalwarsu yanzu babu abinda ta ke buƘata sai hutu da fatan cikawa da imani ga ma su hankali da hangen nesa na cikinsu.

By ukarofi