An buƙaci Tinubu ya shawo kan tsadar fetur da lantarki don magance hauhawar farashi

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Masu sayar da kayan abinci da su ka haɗa da manyan da ƙananan ’yan kasuwa sun yi kira ga Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da ta sanya tsarin da zai shawo kan matsalar farashin man fetur da dizal da wutar lantarki domin a samu raguwar farashin kayan abinci.

Binciken da jaridar Blueprint ta yi ya nuna yadda ‘yan kasuwa mata da maza ke ƙorafi ba wai kawai a kan hauhawar farashin man fetur ba, amma da ƙarancin kayan masarufi.

Sun ba da misali da simintin BUA da kamfanin ke sayar da shi akan Naira 3,500, amma ana sayar da shi a kan kusan Naira 8,000 a kasuwa, duk saboda kayan aikin sufuri, ciki har da shingen bincike da yawa a kan tituna.

Wani mai sayar da albasa, Ismalia Yusuf, ya ce ba don farashin man fetur da dizal ba, da farashin kayanya daidaita a Legas.

A cewar Yusuf, farashin buhun albasa ya kai kusan N160,000 ko sama da haka a Legas, amma a arewa ya ragu sosai, ya ƙi bayyana haƙiƙanin farashin buhun albasa a Arewa.

Wata mace kuma da ta je Binuwai don sayen doya, kasuwannin a yankin kudu maso yamma, sun zargi man fetur, dizal da kuma shingayen binciken ababen hawa na doka da na waɗanda ba na doka ba, da ƙara saka farashin abinci ya yi tsada.

By ukarofi