Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Hukumar da ke Kula da Kasuwar Hannayen Jari a Nijeriya, SEC, ta ba da damar musayar kuɗin crypto ga wasu kamfanoni biyu, don fara aiki a ƙarƙashin tsarin ARIP.
Efe Ebelo, kakakin hukumar ne ta sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Legas.
A cewar Ebelo, kamfanonin da aka bai wa izinin su ne Busha Digital Ltd, da ƙuidaɗ Technologies Ltd.
Ta ce, amincewar ya kasance ne don ci gaba da ƙudurin SEC na ba da damar ƙirƙire-ƙirƙire da za su zurfafa kasuwar jari tare da ba da tabbacin kare masu zuba jari.
