NNPC zai iya kasa shigo da fetur saboda hauhawar farashi

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Farashin man fetur na iya tashi sama da Naira 1,000 a kan kowace lita a gidajen mai saboda an ƙara farashin kayan kayayyaki a wasu gidajen mai masu zaman kansu zuwa tsakanin N920 zuwa N950 a lita.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da masu zanga-zangar suka mamaye titunan Abuja a ranar Litinin ɗin da ta gabata, inda suka buƙaci da a gaggauta korar Manajan Darakta na Kamfanin Man Fetur na Nijeriya Mele Kyari, sakamakon ƙarancin man fetur da ake fama da shi a ƙasar.

An tattaro cewa kamfanin mai na ƙasa NNPC ya sanar da ‘yan kasuwar mai game da matsalar kuɗi dangane da shigo da mai.

Hakan dai ya tayar da hankulan dillalai, inda suka nuna damuwarsu kan yiwuwar dakatar da shigo da mai da kamfanin na NNPC ke yi.

A baya mai magana da yawun kamfanin NNPC Olufemi Soneye, ya bayyana cewa kamfanin mai na kasa na fuskantar matsalar kuɗi. NNPC shi ne kaɗai mai shigo da man fetur cikin Nijeriya, tare da bayar da tallafi ga kayayyakin da ke gudana zuwa tiriliyan nairori da dama.

“NNPC na fuskantar matsalar kuɗi saboda tsadar kayan man fetur, yana tasiri ɗorewar wadata. Kamfanin mai na NNPC ya amince da rahotannin baya-bayan nan a jaridun ƙasar nan dangane da ɗimbin basussukan da kamfanin ke bin masu samar da mai. Wannan matsalar kuzi ta sanya matsi mai yawa a kan kamfanin tare da yin barazana ga ɗorewar samar da mai.

A cikin makon nan Kamfanin mai na Nijeriya, NNPC ya sanar da sabon farashin litar man fetir. A wata sanarwa da kamfanin ya aike wa manema labarai, kamfanin ya ce daga yau ranar 3 ga watan Satumban 2024, kamfanin ya ƙara kuɗin litar man fetir daga naira 617 zuwa 897.

Tuni dai wasu gidajen mai a Nijeriya suka sauya farashin litar zuwa sabon da kamfanin ya sanar a ranar ta Talata.

Wannan dai na zuwa ne kwana ɗaya bayan da kamfanin na NNPCL ya bayyana cewa yana fuskantar matsalar ƙarancin kuɗi, wani abu da ya sa ‘yan Nijeriya hasashen kamfanin na ƙoƙarin sanar da sabon farashi ne.

Da ma dai kafin sanar da sabon farashin na ranar Talata, dogayen layukan ababan hawa sun mamaye gidajen mai a biranen Abuja da Legas.

Tun dai bayan da gwamnatin shugaba Tinubu ta sanar da janye tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayun 2023, ’yan Nijeriya ke fuskantar sauye-sauye a farashin man wanda kuma ke taɓa sauran sassan rayuwa.

Sai dai kuma, gwamnatin tarayya ta musanta bai wa kamfanin umarnin ƙara farashin litar mai ɗin.

By ukarofi