A safiyar jiya Lahadi, wata tankar mai ta fashe a kan hanyar Lapai- Agaie da ke ƙaramar hukumar Agaie a Jihar Neja.
Lamarin ya faru da safiya wajen ƙarfe 12:30 inda motar shaƙare da mai tai arangama da wata motar fasinja mai ɗauke da shanu.
Motar ɗauke da shanu ta taso ne daga Wudil Jihar Kano za ta wuce Legas in da tai karo da tankar man a Jihar Neja.
Wasu motoci guda biyu da ke kusa su ma sun ƙone ƙurmus a dalilin tashin wutar.
Rahotannin sun nuna cewa aƙalla mutum 48 ne suka rasa rayukan su da aƙalla shanu 50. Waɗanda su ka rasa rayukan su tuni an yi jana’izar su kamar yadda musulunci ya tsara.
Gwamnan Jihar Neja ya miƙa ta’aziyar shi ga waɗanda suka rasa rayukan su, kuma ya bayyana gwamnati na baƙin ƙoƙarin ganin ta shawo kan lamarin cikin gaggawa.
Shima shugaban hukumar bada agajin gaggawa na Jihaf Neja, Abdullahi Baba-arah ya tabbatar da sun aika da jami’an gaggawa domin shawo kan lamarin.
