An kafa kwamitin bikin cika shekaru 37 da ƙirƙiro Jihar Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina.

Gwamnan Jihar Katsina malam Dikko Raɗɗa ya bada umarnin kafa kwamitin da zai shirya bikin cika shekaru 37 da ƙirƙiro Jihar Katsina.

Sakataren gwamnatin jihar Abdullahi Garba Faskari da shine zai kasance shugaban kwamitin ya bayyana haka a hira da manema labarai a ofishin sa.

Sauran mambobin kwamitin kamar yadda ya faɗa sun haɗa da shugaban ma’aikata na gidan gwamnatin Katsina Alhaji Jabiru Tsauri da kwamishinan Shari’a.

Sauran sun haɗa da Kwamishinonin yaɗa labarai da al’adu da na ayyuka da gidaje da sufuri, harkokin mata da ƙasa da tsare tsaren birane da wasu manyan jami’an gwamnati.

Wasu daga cikin aikin kwamitin Kamar yadda sakataren gwamnatin ya faɗa shine tsara ƙasaitaccen biki da gayyatar manyan mutane.

Tsohon shugaban ƙasa Ibrahim Badamasi Babangida ne ya ƙirƙiro jihar a ranar 23 ga watan Satumba a 1987 wanda a koda yaushe a wanann rana ana tunawa da ita.

By ukarofi