PDP ta soki Tinubu kan kama shugaban NLC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Jam’iyyar PDP ta soki Shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda kama ƴan Nijeriya da jami’an tsaro suke yi.

A yau Litinin ne jami’an hukumar ƴan sandan farin kaya, DSS suka kama shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC), Joe Ajaero a Filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja..

Sakataren yaɗa labarai na ƙasa a jam’iyyar, Debo Olugunagba ya ɗora wa Tinubu laifin kakkama mutane da aka yi, musamman la’akari da kama shugaban ƙwadago da aka yi a yau, ya na mai bada tabbacin cewa za su jira su ga abin da zai biyo bayan haka.

A watan da ya gabata ne aka gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya inda aka kama mutane da dama.

Olugunagba ya ce, “akwai buƙatar a kula. Akwai zanga-zangar da aka yi a ƙasar nan. Gwamnatin babu abin da ta yi. Kun kama mutane kuma kun ce ƴan ta’adda ne, sannan kun kai su kotu. Kun ce wasu mutane ne suka ɗauki nauyin zanga-zangar.”

Ya ce, wacce ta ɗauki nauyin zanga-zangar ita ce yunwa, ya na mai ce wa Shugaba Tinubu da mutanesa su kama yunwa don haka sai a yi shuru da batun.

Ya ƙara da cewa, tsare-tsaren Tinubu su na da tsauri ta yadda su ke sanya al’umma cikin ƙunci wanda a sakamakon haka ba sa iya tsara yanayin gudanar da al’amuransu na yau da kullum.

Ya kuma ce, ana yin gwamnati ne don walwalar al’umma da samar musu da tsaro, ya na mai cewa, a wannan gwamnatin babu ɗaya daga ciki da ke samuwa.

Bugu da ƙari, matuƙar gwamnati ta samar da walwala ga al’umma, to babu zanga-zanga da za sake yi.

Kazalika, ya bayyana cewa, “wannan ƙasa ce da ba za ta iya biyan mafi ƙarancin albashi na N70,000 ba inji su. Amma ƙasa ce da za ta iya sayen jirgin sama na Dala miliyan 150.

By Babaji