
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa, NLC ta gudanar da wani zama na gaggawa sakamakon kama shugabanta, Joe Ajaero da jami’an hukumar DSS suka yi a yau Litinin, a filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja.
Jami’an sun kama Ajaero ne akan hanyarsa ta ficewa daga Nijeriya zuwa Burtaniya don halartar taron Ƙungiyar Kasuwanci (TUC).
A yayin zaman ne shugabannin NLC suka cimma ababe kamar haka; na farko, a gaggauta sako shugaban nata a yau da aka kama shi kafin karfe 12 na dare.
Na biyu, a dawo da farashin litar man fetur zuwa N617 kamar yadda ya ke a baya.
Na uku, NLC ta sanar da dukkan rassanta na jihohi da ƙungiyoyi masu zaman kansu da al’ummar ƙasa su kasance cikin shiri.
Sannan na huɗu, ta kira taron gaggawa na Majalisar Zartarwar ta Ƙasa, NEC da za a yi a gobe wanda za a fara da misalin ƙarfe 9 na safe – 10 ga watan Satumba, 2024.
