Bayan kama Ajaero, DSS sun afka ofishin SERAP a Abuja

Spread the love

Daga USMAN KAROFI a Abuja

Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun mamaye ofishin SERAP a Abuja.Wannan ya zo ‘yan sa’o’i bayan jami’an DSS sun kama Joe Ajaero, shugaban Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa.

Cikakkun bayanai game da abinda ya faru a ofishin SERAP har yanzu ba a samu ba, amma a cewar wani rubutu a X, hukmar ta nemi ganin darakticin Ƙungiyar.

Sai dau rubutun ya cigaba da kira ga shugaba Tinubu ya umarci DSS ta dakatar da tsoratarwa da kuma kai hari kan haƙƙin ‘yan Najeriya,” in ji rubutun.

In bamu manta ba, a ranar Lahadi, SERAP ta ba Shugaba Tinubu awanni 48 don ya janye ƙarin farashin man fetur da aka yi.

By ukarofi