Shugaban NLC da aka tsare na fuskantar tuhume-tuhumen laifuka daban-daban

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Alamu masu ƙarfi na nuna cewa shugaban ƙungiyar ƙwadago, Joe Ajaero zai fuskanci tuhume-tuhumen laifuka daban-daban ciki har da na tilasta karɓar kuɗaɗe ba bisa ka’ida ba, zarginsa da haɗa baki da wasu da ake nema ruwa a jallo da kuma tsauri wajen mu’amalantar hukumomin tsaro.

Wani sahihin binciken sirri ya bayyana cewa, waɗannan dalilai na daga cikin ababan da suka sanya kama Ajaero da hukumar DSS ta yi a jiya Litinin. Lamarin da ya auku a lokacin da ya nufi Landan don halartar taron Ƙungiyar Kasuwanci (TUC) a Burtaniya.

Ɗaya daga cikin manyan ababen da ake zargin Ajaero da su shine, ya na karɓar kuɗaɗe daga ƴan kasuwa da dama da ofisoshi. Cikin waɗanda suka shigar da ƙara akwai ‘Air Peace’ wanda an miƙa wa hukumar da ta dace don ji da batun.

Abin da ake tuhumar sa akai ya kai ga wuce gona da iri wanda ana ganin ba huruminsa ba ne a matsayinsa na shugaban NLC.

Wani bincike da Hukumar Leƙen Asiri (NIA) ta yi, ya mayar da hankali kan yadda Ajaero ke alaƙa da wani ɗan ƙasar waje da ake neman sa ruwa a jallo kasancewar ana tuhumar sa da laifukan da suke barazana ne ga zaman lafiyar Nijeriya.

Wani babban jami’in tsaro ya bayyana halin Ajaero a matsayin girman-kai da kuma abin da jami’an tsaro ba za su amince da shi ba, ya na mai cewa ya kan nuna kamar ya fi ƙarfin a taɓa shi ko a yi bincike akan sa.

Ya ce, Ajaero ya sha yin buris da gayyatar hukumomin tsaro wanda ake ganin hakan a matsayin rashin girmamawa ce a gare su.

Rahotonni sun bayyana cewa, duk da ƙoƙarin siyasantar da lamarin da NLC ke yi, hakan bai sa jami’an sun daina tirjewa akan cewa matsala ce ta kai-da-kai ba.

Hakan kuma wata majiya ta ce, al’amarin bai shafi NLC ko ma’aikata ba, ta na mai cewa al’ummar Nijeriya ba a ƙarƙashinsa su ke ba da za a yi barazanar shiga yajin aiki.

Kawo yanzu dai, DSS ta sako Ajaero a daren da ya biyo bayan ranar da ta kama shi tare da ƙwace masa fasfo wanda hakan ke nuna cewa har yanzu ana cigaba da gudanar da bincike akan sa.

By Babaji