Ajaero bai fi ƙarfin doka ba – Fadar Shugaban Ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Offishin shugaban ƙasa ya kare maganar kama shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) Joe Ajaero inda ya ce bai fi ƙarfin dokar ƙasa ba.

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga ya faɗi hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

A ranar Litinin ne jami’an DSS suka kama Ajaero a Filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja a lokacin da ya nufi Burtaniya wanda sai bayan sa’o’i 15 ne suka sako shi.

Hakan ya haifar da cecekuce acikin al’ummar ciki da wajen Nijeriya da ma ƙungiyoyi masu zaman kansu waɗanda suka zargi gwamnati da tozarta shugabanci da kuma tauye haƙƙin ɗan-adam.

Ɗaya daga cikin misalan shi ne tsokacin da aka gani na babban sakataren Ƙungiyar Kasuwanci (TUC) ta Burtaniya, Paul Nowak da ya yi game da batun inda ya ce sako shi da aka yi a ranar da aka kama shi ya nuna ba a kammala al’amarin ba, kuma hakan ba bisa ƙa’ida ba ne don ya tauye ƴancinsu na ƙungiyar ƙwadago kasancewar akan hanyarsa ta zuwa tattaunawa da su aka kama shi.

Ya ce, za su cigaba da bai wa ƙungiyoyin ƙwadago na Nijeriya goyon baya tare da yin watsi da matakin gwamnatin tarayya sannan ya yi kira gare ta da ta ƙaurace wa gudanar da bincike akan Ajaero.

To sai dai, Onanuga acikin saƙon da ya fitar, ya ce gwamnati ba ta kama Ajaero ba tare da dalili ba, ya na mai cewa shugaban ƙwadagon ya ƙi amsa gayyatar hukumar ne.

Ya ce, Ajaero mutum ne wanda ya ke ji kamar ya fi ƙarfin doka kuma an zaɓe shi a matsayin wanda zai tattauna a irin taron da ya soki Nijeriya yayin da babu wanda ya fi ƙarfin doka a Nijeriya.

Ya ƙara da cewa, gogaggen ɗan siyasa ke jagorantar Nijeriya wanda zai yi duk abin da ya dace don walwalar al’ummarsa da kuma tabbatar musu da ƴancinsu.

Onanuga ya ce, yayin da gwamnatin da ƙungiyoyin ƙwadago ke samun saɓani wajen tattauna batutuwan da suka shafi al’ummar ƙasa, hakan ba shi ke nuna akwai takun-saƙa a tsakaninsu ba da zai ka ga sanya takunkumi wa jami’ansu.

By Babaji