Daga UMAR GARBA a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina Dikko Umar Raɗɗa, ya mayar da martani ga masu sukar gwamnatinsa bayan da gwamnatin ta buƙaci al’umma su kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga.
A cewar Raɗɗa, kiran al’uma su yi fito na fito da ‘yan ta’adda ba kasawa ba ce daga gwamnati.
“Ba kasawa ba ce, banda soja banda ɗan sanda, a matsayina na gwamna na yi abinda zan iya yi, na ɗauki matasa, na horar da su na ba su makamai na ba su motoci da babura don su samar da tsaro,” inji shi.
Gwamnan ya ce, yana takaicin yadda ‘yan bindigar da ba su wuce mutum biyar ko goma ba ke tarwatsa gari guda, a cewar shi idan al’ummar jihar suka cire tsoro za su iya kama su da hannu.
“Idan matasa ɗari suka yunƙura suka nufi ‘yan bindigar ko sun kai mutum 20 da sun fara harba bindiga ɗaya, biyu kafin su yi harbi na biyar an kama su da hannu,” inji Raɗɗa.
Ya kuma ce, dalilin da ya sa gwamnatin jihar ta buƙaci al’umma su yi fito na fito da’yan ta’addar saboda babu wadatattaun jami’an tsaro a ƙasar nan da za su iya kare su.
“A jihar Katsina akwai ƙaramar hukumar da take da ‘yan sanda 32, sannan bindigoginsu mafi kyau guda biyar ne kaɗai, yanzu don girman Allah ƙaramar hukumar dake da ƙauyuka kusan ɗari uku ta ya ‘yan sanda 32 za su tsare su?” Kamar yadda gwamnan ya tambaya.
“Saboda haka al’umma su haɗa kansu za mu horar da matasa mu ba su bindigogin da hukuma ta yarda a ba su, idan sun ga ‘yan ta’adda su fito su tsare iyalansu kafin ma su kira jami’an tsaro,” inji shi.
A cewar gwamna Raɗɗa, ƙin yin fito na fito da ‘yan bindigar bai hana ɓarayin yin garkuwa da mutane ba ko ma a kashe su wani lokaci.
