Gidauniyar Musulunci ta Malam Inuwa Dutse ta yaye ɗalibai 30 da suka sauke Alƙur’ani cikin shekara ɗaya

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An yaye ɗalibai 30 da suka yi saukar Alƙur’ani a cikin shekara ɗaya a karo na farko  a ƙarƙashin Gidauniyar Musulunci ta Malam Inuwa Dutse.

Da yake zantawa da ‘yan jarida a yayin bikin saukar. Darakta Janar na biyu na gidauniyar, Ambasada Hon. Usman Inuwa Dutse ya ce lokacin da suka ƙaddamar da buɗe gidauniyar Musulunci  ta Malam Inuwa Dutse a ranar an buɗe masallacin Juma’a.

Ya ci gaba da cewa ana sallar Idi a masallacin da duk wani abu da ya shafi addinin Musulunci, sannan sai suka yi tunanin cewa ya kamata su ɗebi yara a koya musu yadda za su sauke ƙur’ani a cikin shekara ɗaya kyauta.

Ya ce yaran su  34 aka ɗauka aka soma da su aka raba su ajijuwa a cikinsu guda  30 ne suka sauke sune aka yi bikin saukarsu tare da da buɗe makaranta da aka gina aka sa mata suna “Inuwa Dutse International School” wacce ta ilimin zamani ce da haddar ƙur’ani da Islamiyya. Dama ce da za a bai wa yara su zo su yi karatun ƙur’ani da za su sauke a shekara.

Hon. Ambasada  Usman Inuwa Dutse wanda shi ma ɗaya ne daga ‘ya’yan Marigayi Malam Inuwa Dutse sannan shi ne mai bai wa Gwamnan Jihar Jigawa Malam Umar Namadi Danmodi shawara na musamman akan “Inɓestment Promotion” ya ce dukkan ɗawainiyar koyar da  ɗaliban da suka sauke kyauta ne. A lokacin da suka yi niyyar gina cibiyar da masallacin sun ƙudurce Allah ne zai musu kuma ya ba su iko aka yi cikin nasara.

Ya bayyana karramawa da ƙungiyar iyayen yara na makarantar da  suka yi saukar suka yi musu da lambobin yabo da cewa abin jin daɗi ne, su dama cibiyar an samar da ita ne domin al’umma. Kuma su iyalan Malam Inuwa Dutse irin tarbiyya da aka yi musu kenan a gidansu suke cigaba da  ɗorawa a kai kuma mutane sun shaida cewa ana basu gudunmawa.

Ya ce a cibiyar ta Malam Inuwa Dutse suna abubuwa da yawa da suka haɗa da yin kaciya ga yara an yi wa yara 75 a baya sun ma  gina asibiti a harabar cibiyar da za a buɗe nan bada jimawa ba, akwai gidan liman da wajen wanke mamaci da gidan ladan da masaukin baƙi.

Ya ƙara da cewa irin cuɗanya da suke da mutane ne tasa suke fahimta da sanin  buƙatunsu  babu kuma abinda ya fi ka ba mutane ilimi na addini dana zamani da shine ginshiƙi na gina rayuwa mai kyau.

Hon. Ambasada Usman Inuwa Dutse ya ce makarantar da aka buɗe ta zamani ce da ta ƙunshi duk abinda ɗalibi yake nema na samun ilimi an tanade shi. Sannan sun ɗan saka ‘yan kuɗi da iyaye za su riƙa bayarwa, domin su jawo hankalinsu wajen bayar da himma akan abinda ake yi,  yanzu akwai malamai 14 a makarantar kuma suna sa ran samun ɗinbin ɗalibai.

Taron dai ya samu halartar mutane da dama daga cikin da wajen Kano cikin waɗanda aka karrama a yayin bikin saukar sun haɗa da Alhaji Aminu ɗantata wanda ɗansa Alhaji Tajuddeen ya karɓa a madadinsa da Darakta Janar na Gidauniyar Malam Inuwa Dutse ɗansa Dakta Abdullahi Inuwa Dutse da Darakta Janar na biyu, Ambasada Hon. Usman Inuwa Dutse da Alhaji Muhammad Isma.

By ukarofi