Al’ummar ƙaramar Hukumar Fagge sun roƙi Tinubu ya naɗa Abdul’azeez Abdul’azeez a matsayin kakakinsa

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Al’ummar ƙaramar Hukumar Fagge da masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC  a ƙaramar hukumar sun yi kira ga Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu akan ya maye gurbin Ajuri Ngalale da ya ajiye aiki na mai magana da yawun shugaban ƙasa a kwanakin baya da ɗansu mataimaki  na musamman ga shugaban ƙasar akan kafafen yaɗa labarai Malam Abdulaziz Abdul’azeez.

A wata sanarwar bayan taron da masu ruwa da tsaki na Fagge suka gudanar da shugaban matasa APC  na ƙaramar hukumar Musa Rabiu Fagge ya yi jawabi a madadinsu ya nuna cewa Malam Abdul’azeez  ɗan asalin ƙaramar hukumar ne yana da kyakkyawan hali da ladabi da biyayya da taimakon al’umma.

Ya ƙara da cewa Abdul’azeez Abdul’azeez haziƙin ɗan jarida ne mai ƙwazo da yake gudanar da aikin da shugaban ƙasa Bola Tunubu ya ba shi yadda ya kamata.

Ya ce irin ƙwarewarsa da gogayya da yake da ita zai iya riƙe wannan muƙami na mai magana da yawun shugaban ƙasa cikin nasara ya kare kimar wannan gwamnatin tarayya.

Shugaban matasan na jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Fagge, Musa Rabiu ya ce Malam Abdul’azeez ɗan jarida ne da ya fara aiki tun daga mai ɗauko rahoto har zuwa edita,  ya yi aiki a manyan jaridun Nijeriya daban-daban da ya samu lambobin yabo da yawa.

A ƙarshe shugaban matasan na jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Fagge Musa Rabiu Fagge ya jaddada kira ga shugaban ƙasa Ahmad Bola Tunubu akan za su yi matuƙar farin ciki idan ya baiwa ɗansu Abdul’azeez Abdul’azeez wannan matsayi na mai magana da yawunsa kuma suna tabbatar masa da cewa zai kare masa kima da mutuncin gwamnatinsa a tsakanin ‘yan Nijeriya.

By ukarofi