Samar da zaman lafiya da tsaro aikin kowa ne

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Ranar 7 ga watan Satumba na kowacce shekara za ta cigaba da kasancewa rana mai muhimmanci a rayuwar ‘yan Nijeriya, musamman mazauna Jihar Filato, sakamakon mummunan rikicin da ya ɓarke a garin Jos wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiyoyi da dama. Kamar yadda ranar 11 ga watan Satumba take da muhimmanci a tarihin ƙasar Amurka, saboda harin da aka kai kan Cibiyar Kasuwanci ta Duniya (WTC).

Babu shakka ba al’ummar Filato kaɗai ba, duk wani ɗan Nijeriya da ke da ɗan uwa a Jos, ba zai manta da wannan rikici ba, wanda aka alaƙanta shi da addini da siyasa. Shekaru 23 bayan faruwar wannan al’amari, har yanzu Jihar Filato ba ta koma daidai yadda take a baya ba, duk da ƙoƙari da gwamnatocin baya da jami’an tsaro, shugabannin al’umma, ƙungiyoyin matasa da masu aikin sakai, har da ƙungiyoyin ƙasashen waje masu ba da tallafi, suka riƙa yi. Ko kuma za a iya cewa, har yanzu ma suke kan yi. Kodayake ana samun cigaba sosai a yanayin zamantakewa da mu’amala ta yau da gobe.

Amfani da siyasa da hare-haren ’yan ta’adda kan mazauna karkara, rikicin manoma da makiyaya, da ayyukan ‘yan bindiga masu satar shanu da garkuwa da mutane don karɓar kuɗin fansa, na daga cikin matsalolin da suka riƙa haifar da koma-baya ga cigaban jihar. Sai dai matakan da gwamnati, jami’an tsaro, da ƙungiyoyin sakai suka riƙa ɗauka lokaci zuwa lokaci, wajen shirya taruka na wayar da kai, haɗa gwiwa tsakanin al’ummomin da ke gaba da juna, gudanar da wasan ƙwallon ƙafa, da ziyarar juna don ƙarfafa zumunci, ya taimaka wajen dawo da yarda da juna, zaman tare, da inganta zaman lafiyar da ake cin moriyarsa a halin yanzu.

A yayin da ake duba nasarori da ƙalubalen da rashin zaman lafiya ya kawo wa Jihar Filato, wata ƙungiya da ta yi fice wajen ayyukan samar da zaman lafiya da inganta tsaro a jihar, ita ce ƙungiyar Centre for Community Actions for Peace and Deɓelopment, wacce ake yi wa laƙabi da CCAPAD. Wannan ƙungiya tare da haɗin gwiwar wasu ƙungiyoyin al’umma da suka haɗa da ƙungiyoyin addini, ’yan banga, sarakuna, wakilan gwamnati a matakin ƙananan hukumomi, ƙungiyoyin mata da matasa, da nakasassu, har da masu wakiltar manoma da makiyaya, sun gudanar da wani aiki na tsawon shekaru biyar, a jihohin Filato, Bauchi da Adamawa, da nufin koyawa jama’a muhimmancin zaman tare, da yaƙi da ɓata-gari masu fakewa da bambance-bambancen da ake da su suna haifar da fitina da rashin tsaro.

A wani taro da ƙungiyar ta kira a Jos, wanda na samu halarta, albarkacin zagayowar ranar 7 ga watan Satumba, na samu damar ganawa da wasu masu ruwa da tsaki, da suka ba da gudunmawa a yankunansu domin samar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma. Sun kuma ba da shaida kan irin rawar ganin da wannan ƙungiya ta taka ta fuskar sasanta matsalolin manoma da makiyaya, yaƙi da matsalar matasa masu shaye-shaye, da haɗin gwiwa da hukumomi da jami’an tsaro wajen sa’ido kan baƙi masu shige da fice, don magance matsalar masu satar mutane su yi garkuwa da su.

Duk da kasancewar bayan mummunan rikicin 7 ga watan Satumba na shekarar 2001, an fuskanci wasu ƙarin fitintinu da suka auku a cikin garin Jos da ƙauyukan Jihar Filato, masu nasaba da ƙabilanci da addini. Wannan ce ta sa har a lokacin gwamnatin tsohon Shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo cikin shekarar 2004, aka sanyawa jihar ‘Dokar Ta ɓaci’, domin ɗaukar matakan tsaro masu ƙarfi da za su dakatar da asarar rayuka da dukiyoyi da aka fuskanta.

Gwamnatoci daban-daban da aka yi a jihar sun yi ta nasu ƙoƙarin don ganin sun gyara tafiyar al’amura, wanda har ta kai ga kafa Hukumar Bunƙasa Zaman Lafiya ta Jihar Filato, da ta yi ta faɗi tashin ganin ƙalubalen tsaro a tsakanin manoma da makiyaya a lunguna da ƙauyukan jihar sun kau.

Yanzu za a iya cewa, Jihar Filato ta hau sabon ƙadami, a matsayin jihar da jama’a ke rubibin zuwa don hutawa da kasuwanci, saɓanin yadda a baya aka ƙauracewa jihar saboda matsalolin tsaro da rikice-rikice da suka addabeta. An gudanar da zaɓukan ƙananan Hukumomi da na Kansiloli cikin cikin lumana, saɓanin a shekarun baya, wanda da zarar an ce za a yi zaɓe irin wannan hankalin jama’a tashi yake yi. Hakan na faruwa ne sakamakon mummunan rikicin da aka yi a shekarar 2008, bayan sakamakon zaɓen da ake kan tattarawa ya nuna wasu da ba a son ganin sun riƙe madafun iko a jihar su ne suke da rinjayen ƙuri’u.

Shugaban ƙungiyar CCAPAD, Ahmad Auwalu Salihu ya bayyana cewa, sadaukarwa da jajircewar mambobin su, masu faɗa a ji da malaman addini, sun taimaka sosai wajen samar da ingancin zaman tare, ba kawai a zauna tare irin zaman doya da manja ba, a samar da amincewa da yarda wacce a baya aka san Hausawa, Fulani da sauran ƙabilun Filato suna yi.

Ya ƙara nuni da cewa, duk da ƙalubalen tsaro na ta’addanci da yake canza salo lokaci zuwa lokaci, ƙungiyar CCAPAD da sauran ƙungiyoyin sakai masu aikin samar da zaman lafiya, sun yi ƙoƙari wajen ɗinke ɓarakar da ake samu. Kuma ƙoƙarin da suke yi ne ya sa ko an samu wata fitina ta taso, nan da nan ake iya shawo kanta, ba tare da ta yi tasiri sosai ba, saɓanin yadda a baya ake samun asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa.

Yana da muhimmanci gwamnati mai ci a Jihar Filato ta fahimci ƙalubalen da ke gabanta wajen tabbatar da ɗorewar zaman lafiyar da aka wahala sosai wajen samar da shi. Sannan ta mara wa ƙungiyoyi irinsu CCAPAD baya don ganin sun taimaka mata, tare da Hukumar Bunƙasa Zaman Lafiya ta Jihar Filato, domin ganin duk wani ɓurɓushin rashin yarda, rashin cigaba, ayyukan tsagerun matasa. A kula sosai don ganin ayyukan shugabanni, malaman addinai, da ’yan siyasa masu fakewa da addini ko siyasa suna haifar da rabuwar kai ko rashin zaman lafiya, saboda son zuciyarsu, basu samu yadda suke so ba, kuma doka ta yi aikinta kan duk wanda aka lura ba mai son zaman lafiya ba ne. 

A yanzu da ake shirye-shiryen zaɓukan ƙananan hukumomi a jihar, lallai ne al’ummar Filato su zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya, su haɗe kansu, kuma su bai wa mara ɗa kunya, don ganin abubuwan da suka faru a baya ba su sake faruwa ba. CCAPAD da abokan hulɗarta su ma su ƙara jan ɗamara don ganin sun ƙara faɗakar da jama’a muhimmancin yin siyasa ba da gaba ba, kuma a yi zaɓe cikin lumana. Duk wanda Allah Ya bai wa nasara ya ja kowanne ɓangare a jikinsa don a gudu tare a tsira tare.

By ukarofi