Daga AISHA ASAS
Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai na Jihar Kano Alhaji Abba El-mustapha, ya jaddada alƙawuran gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf na wadata masana’antar finafinan kannywood da dabarun zamani a harkar fim.
Abba El-Mustapha ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da fom 100 na koyar da aikin fim ga ‘yan Masana’antar Kannywood na shirin horarwa na tsawon watanni biyu kan harkar fim da kasuwanci, wanda Cibiyar FinaFinai ta Jihar Kano za ta gudanar.
Abba El-mustapha ya bayyana cewa shirin wani ɓangare ne na ƙoƙarin da gwamnatin Jihar Kano ke yi na bunƙasa fasahar ‘yan masana’antar Kannywood, da samar musu da dabarun shirya finafinan zamani, da ka’idoji, da dabarun kasuwanci don bunƙasa dogaro da kai.
Ya kuma ƙara da cewa, shirin na da nufin bai wa mahalarta taron ilimi da kayan aikin da suka dace don samun nasara a masana’antar finafinai masu tasowa. Ya kuma buƙaci ɗaukacin mahalarta taron da su yi amfani da wannan dama mai amfani da gwamnatin Jihar Kano ta ba su, inda ya jaddada muhimmancin bayar da horon domin ciyar da sana’ar su gaba da kuma ba da gudunmawa ga ci gaban masana’antar finafinai ta cikin gida.
“Manufar wannan horon ita ce faɗakar da masu shirya finafinan namu da ayyukan zamani da ka’idoji, ta yadda za su kasance masu dogaro da kai da samun nasara a harkokinsu,” inji Abba El-mustapha.
A ƙarshe ya yaba da gagarumin goyon baya da haɗin kai daga gwamnati wajen aiwatar da shirin da sauran tsare-tsare da ke amfanar masana’antu.
A nasa jawabin shugaban ƙungiyar ‘yan wasa na Jihar Kano, Malam Alhassan Kwalle, ya bayyana matuƙar godiya ga gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa jajircewarsa na inganta masana’antar a jihar.
“Muna godiya ga Gwamna Yusuf da ya ɗauke mu a matsayin waɗanda suka cancanci wannan damar don inganta ƙwarewarmu kuma tare da horon da aka ba mu, muna da tabbacin cewa mambobinmu za su iya yin gogayya da takwarorinsu na duniya.”
