Kwanan nan ma’aikata za su fara cin gajiyar sabon mafi ƙarancin albashi – Gwamnatin Tarayya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnatin Tarayya ta ce kwanan nan ma’aikata za su fara amsar albashi da sabon tsarin mafi ƙarancisa da ƙasa ta amince da shi yayin da ake ƙoƙarin kammala shirye-shiryen hakan.

Ƙaramar Ministar Ma’aikatar Ƙwadago da Ɗaukar aiki, Nkeiruka Onyejeocha ta faɗi hakan yayin wani zama da haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago da ma’aikata a Abuja a ranar Juma’a, wanda aka gudanar da shi don tattauna alƙawuran da gwamnatin Shugaba Tinubu ta yi wa al’umma.

Sannan, an gudanar da zaman ne don ƙarin haske game halin da ake ciki na sabonta ƙasa ga gwamnatin ta yi alƙawarin yi da kuma yaba wa ƙoƙarin ƙwadago da ma’aikata da ake fatan fara biyan su da sabon tsarin da zarar an kammala zaman.

Onyejeocha ta ce, gwamnatin tarayya da kwamitin kula da ma’aikata, da kuma Ma’aikatar Ma’aikata na gudanar da zama a yau don tattauna yadda tsarin biyan zai yi daidai da sabon mafi ƙarancin albashin.

Ministar ta kuma tabbatar da ƙoƙarin gwamnatin tarayya na warware matsalolin zamantakewar al’ummar ƙasa tare da samar da hanyoyin dakatar da waɗanda ka iya tasowa.

By Babaji