Shettima ya ziyarci sansanin ƴan gudun hijira a Neja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Juma’a ne Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya kai ziyara sansanin ƴan gudun hijira na Gwada da ke ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja.

Ya ce, Shugaba Bola Tinubu ya bada umarnin kai ziyarar don duba halin da mutanen da ambaliya da rashin tsaro suka yi sanadiyyar komawarsu wajen da kuma tallafa mu su.

Ya bayyana alhinisa game da rayuka da dukiyoyin da aka rasa yayin aukuwar lamuran, ya na mai jajenta wa ƙananan hukumomi 14 na jihar da hakan suka shafe su.

Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma tabbatar da cewa, gwamnatin Tinubu a shirye ta ke ta bai wa duka jihohin ƙasar taimako inda ya ce an ware Naira biliyan 3 ga kowacce jiha don ji da lamuran ambaliya.

Ya ƙara da cewa, za a yi nazari na musamman ga jihohin da lamuran ambaliya ke cigaba da ɗauɗaita al’umma da yankunansu don ba su cikakken agaji a ƙoƙarin gwamnatin shugaba Tinubu na ji da lamuran al’umma.

Kazalika, Shettima ya yi tsokaci game da hatsarin motar tankar mai da ya yi sanadiyyar rasa rayuka da dama wanda a halin yanzu ana gina titin da lamarin ya auku a ƙoƙarinsu na kiyaye rayuka da dukiyoyin al’umma.

By Babaji