Kotu ta haramta wa Aminu Ado Bayero canza fasalin Gidan Nasarawa

Spread the love

Daga RABIU SUNUSI a Kano

Wata Babbar Kotu Jihar Kano a ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Dije Abdu Aboki, ta bayar da umarnin hana Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, gyaran fadar Nasarawa.

Gwamnatin Jihar Kano, ta hannun babban lauyanta da kuma masarautar Kano ne, suka maka Aminu Bayero a gaban kotun.

Kotun ta bayar da umarnin cewa, dukkanin ɓangarorin da ke cikin wannan shari’a su bar komai yadda yake game da tsarin ginin fadar har sai an saurari ƙarar tare da yanke hukunci.

“An bayar da umarnin wucingadi na hana wanda ake ƙara, wakilansa ko duk wanda ke aiki bisa umarninsa daga rushewa, gyarawa ko sake fasalin ginin Gidan sarki na Nasarawa da ke kan titin zuwa gidan gwamnatin Kano, har sai an saurari wannan ƙara tare da yanke hukunci.”

Takardar kotun, wacce Wakilin Blueprint Manhaja na Kano ya gani, ta nuna cewa, masu ƙarar sun shigar da ƙarar ne a ranar 9 ga watan Satumba.

Ƙarar, wacce mai sakin layi 33 da Matawallen Kano, Alhaji Ibrahim Ahmed, ya sanya wa hannu, kotu ta kuma bayar da umarnin a kai wa wanda ake ƙarar takardun kotu ta wata hanya ta daban tare da tsayar da ranar 2 ga Oktoba, 2024, domin sauraron ƙarar.

Idan za a iya tunawa, a kwanakin baya wasu hotuna suka bayyana a kafafen sadarwa na zamani masu ɗauke sabuwar taswirar zanen sabon fasalin Gidan Nasarawa, wanda ake danganta wa Aminu Ado cewa, yana shirin gyaran ƙaramar fadar ta masaraurar Kano.

A lokacin Blueprint Manhaja ta yi ƙoƙarin jin ta bakin ɓangaren Sarkin Kano na 15 ɗin, amma hakan ya ci tura. Sai dai kuma wata majiya daga fadar Nasarawa ta tsegunta wa Blueprint Manhaja cewa, akwai ƙamshin gaskiya a yunƙurin gyaran Gidan Nasarawa da Alhaji Aminu Ado Bayero ke ƙoƙarin yi.

By ukarofi