Majalisar Wakilai za ta ɗauki mataki kan rashin zartar da umarnin gwamanti na cire manyan makarantu daga IPPIS

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Majalisar wakilan Nijeriya ta ƙudiri aniyar warware ƙalubalen rashin zartar da umarnin shugaban ƙasa na a cire jami’o’i da sauran manyan makarantu daga tsarin biya da bayanan ma’aikata (IPPIS).

Shugaban kwamitin Ilimin Jami’o’in na majalisar, Abubakar Fulata ya faɗi hakan a yayin wani zama na shugabannin jami’o’i a ranar Laraba wanda aka gudanar a Abuja.

Ya ce, Kwamitin na ƙoƙari wajen ganin an warware matsalolin makarantun jami’o’i a Nijeriya.

Ya kuma ce, a halin da ake ciki, Shugaba Tinubu ya amince da cire jami’o’i da manyan makarantu daga tsarin IPPIS da kuma shirya majalisar gudanarwa da hukumomin ilimin manyan makarantu.

Ya bayyana tare da ƙwarin-gwiwa cewa, nan ba da jimawa ba za a warware matsalar umarnin Shugaban ƙasa akan batun, ya na mai nuni da ƙalubale da shugabannin jami’o’i ke fuskanta na hukumomi marasa amfani da ke ƙarƙashin IPPIS kan gudanar da harkokin gudanarwa inda ya bada misali da ɗaukar hayar ma’aikatan da ba malamai ba.

A lokacin da ta ke jawabi game da batun, Farfesa Lilian Salami, wacce ita ce mataimakiyar shugabar jami’ar Benin (VC, UNIBEN) ta ce duk da umarnin shugaban ƙasar, har yanzu jami’o’i sun dogara ne da IPPIS kan lamuran ɗaukar aiki, biyan albashi da sauran harkokin gudanarwa.

A ranar 12 ga watan Yuli ne Majalisar Zartarwa, FEC ta yi umarnin a cire jami’o’in Nijeriya daga daga tsarin IPPIS wanda Shugaba Tinubu ya amince da shi a yayin wani zama kafin sanarwar majalisar.

By Babaji