Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Tsawon shekaru da dama ‘yan Nijeriya sun shaida yadda farashin man fetur ke tashi lokaci bayan lokaci, wanda ya tashi daga Kobo 6 a shekarar 1973 zuwa Naira 897 a 2024 kan kowace lita.
A makon da ya gabata ne Kamfanin NNPCL ya sanar da ƙarin farashin man fetur a ƙasar daga naira 617 zuwa naira 897 kan kowace lita.
Nijeriya dai ce ƙasa mafi arzikin man fetur a nahiyar Afirka, kuma ita ce ta fi kowace ƙasa a nahiyar fitar da man zuwa kasuwar duniya. Lamarin da ya sa da dama ke ganin bai kamata a ce man ya yi tsada a ƙasar ba.
Duk da cewa ba wannan ne karo na farko da aka taɓa yin ƙarin farashin mai a ƙasar ba, matakin ya yi wa ’yan ƙasar raɗaɗi.
Jaridar Blueprint Manhaja, ta kawo tarihin ƙarin farashin man fetur da aka fuskanta a Nijeriya, tun daga shekarar 1973 har zuwa yau (2024).
1973 zuwa 1999: A cikin waɗannan shekaru, man ferur ya kasance da araha fiye da kowane lokaci.
Gowon (1973): Kobo 6 zuwa 8.45 (kashi 40.83)
Murtala (1976): Kobo 8.45k zuwa 9 (kashi 6.5)
Obasanjo (1978): Kobo 9 zuwa 15.3 (70%)
Shagari (1982): Kobo 15.3 zuwa 20 (30.72%)
Babangida I (1986): Kobo 20 zuwa 39.5 (97.5%)
Babangida II (1988): Kobo 39.5 zuwa 42 (6.33%)
Babangida III (1989): Kobo 42 zuwa 60 (42.86%)
Babangida Iɓ (1991): Kobo 60 zuwa 70 (16.67%)
1993-2003: A waɗanan shekaru, an fuskanci canje-canje da dama wanda ya tayar wa ‘yan Nijeriya da hankali a zamanin.
Shonekan (1993): Kobo 70k zuwa Naira 5 (614.29%)
Abacha I (1993): Naira 5 zuwa N3.25 (Farashin ya ragu 35%)
Abacha II (1994): N3.25 zuwa N15 (361.54%)
Abacha III (1994): N15 zuwa N11 (Farashin ya ragu da kashi 26.67)
Abubakar I (1998): N11 zuwa N25 (127.27%)
Abubakar II (1999): N25 zuwa N20 (Farashin ya ragu da lashi 25).
A zamanin Obasanjo zuwa, 1999 zuwa 2007:
Jim kaɗan bayan hawansa mulki, Cif Olusegun Obasanjo ya ƙara farashin man daga naira 20 zuwa naira 30, a ranar 1 ga watan Yunin 2000.
To sai dai a ranar 8 ga watan Yunin 2000 Obasanjon ya rage farashin daga naira 30 zuwa naira 22, wato kimanin ragin kashi 10 cikin 100.
A ranar 1 ga watan Janairun 2002, Obasanjon ya sake ƙara farashin daga naira 22 zuwa naira 26.
A watan Yuni 2003 Obasanjo ya sake aara farashin daga naira 26 zuwa naira 42.
Ranar 29 ga watan Mayun 2004 kuma Cif Obasanjo ya mayar da farashin man naira 50. ƙarin kashi 19.05%.
Ranar 25 ga watan Agustan 2004 ya sake ƙara farashin zuwa naira 65.
ƙarin farashin mai na ƙarshe da Obasanjo ya yi shi ne na ranar 27 ga watan Mayun 2007, inda man ya koma naira 75, ƙarin kashi 15.38%.
Zamanin ’Yar’adua, 2007 zuwa 2009:
Marigayi Umaru Musa ‘Yar’aduwa ya rage farashin mai daga naira 75 zuwa 65 a watan Yunin 2007.
Marigayin ne kaɗai wanda bai ƙara farashin man fetur ba cikin shugabannin da suka mulki Nijeriya tun daga 1973.
Zamanin Jonathan, 2009 zuwa 2015:
A ranar 1 ga watan Janairun 2012 Goodluck Jonathan ya yi ƙoƙarin ƙara farashin zuwa tsakanin naira 138 da naira 250, amma daga bisani ya tsaya a kan naira 97, sakamakon zanga-zangar nuna adawa da matakin.
Zamanin Muhammadu Buhari, 2015 zuwa 2023:
ƙarin farashin mai na farko da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi, shi ne ba da damar sayar da man a kan naira 87 da kobo 50 a gidan man ‘yan kasuwa kodayake farashin bai sauya ba a gidajen man NNPC.
Tun daga wannan lokaci ba a sake samun ƙarin farashin man ba sai a ranar Laraba 11 ga watan Mayun 2016 da gwamnatin Shugaba Buhari ta mayar da shi naira 145.
A watan Maris 2020, faɗuwar darajar fetur a kasuwar duniya ta sake tilasta wa gwamnatin rage kuɗin man daga N145 zuwa N125.
Bayan wata guda, a karo na biyu a watan Mayun 2020, hukumar ƙayyade farashin albarkatun man fetur ta PPPRA ta sanar da sabon farashi daga N121.50 zuwa N123.50 a kowane lita.
Sai a watan Nuwamban shekarar farashin ya ƙaru zuwa naira 170.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bar litar mai a kan naira 210 ya zuwa ranar da ya miƙa wa Tinubu mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Zamanin Shugaba Tinubu, 2023 zuwa yanzu:
Tun sanarwar janye tallafi da shugaba Tinubu ya yi a ranar da aka rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa, 29 ga watan Mayun 2023, farashin mai ya yi tashin gwauron zabi a Nijeriya.
Kwanaki kaɗan bayan sanar da matakin, babban kamfanin mai na ƙasar, NNPCL ya sanar da sabon farashin mai na naira 617 a kan kowacce lita wato ƙarin kusan kaso 300 a kan tsohon farashin.
A ranar Talata, 3 ga watan Satumbar 2024, wato kimanin wata 16 bayan hawansa, kamfanin na NNPCL ya sake fito da wani sabon farashin man na naira 897, inda aka samu ƙarin naira 280.
