
Daga BELLO A BABAJI
Kamfanin man fetur na Ƙasa, NNPCL ya ce, ya sayi fetur daga matatar Ɗangote akan N898 kowacce lita yayin ya fara jidon farko a ranar Lahadi.
An ga manyan motocin NNPCL na ɗaukar mai daga matatar wacce ta ke Lekki a jihar Legas a kafafen sada zumunta.
A ranar Asabar ne NNPC ya ce zai tura motoci 100 zuwa matatar don ɗibar zango farko na man fetur mallakarta.
An ruwaito cewa, NNPCL ya sayi kowacce lita ne akan N760 wanda kakakin kamfanin, Olufemi Soneye ya musa, ya na mai cewa N898 suka sayi kowacce lita guda.
