Da Daloli muka sayar mu ku da fetur ba Naira ba – Matatar Ɗangote ga NNPCL

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Matatar mai ta Ɗangote da ke Legas ta musanta sayar wa NNPCL fetur akan N898 kowacce lita.

Cikin wata takarda da Kakakin matatar, Anthony Chiejina ya fitar, ya bayyana iƙirarin kamfanin a matsayin ruɗar da al’umma.

Ya ce, sun samu labarin da aka jingina wa kakakin NNPCL, Olufemi Soneye na cewa wai sun sayar mu su da mai akan N898 kowacce lita wanda ya ce hakan ba gaskiya ba ce.

Ya yi kira ga ƴan Nijeriya su ƙaurace wa bayanin hakan tare da cewa su jira sanarwa ta musamman daga kwamitin da shugaban ƙasa ya naɗa kan sayar da albarkatun mai da kuɗin Naira wanda za a fitar a ranar 1 ga watan Oktoba, 2024.

By Babaji