Trump ya sake tsallake harin harbin bindiga a wani karo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Tsohon shugaban Amurka kuma ɗan takarar shugaban ƙasar, Donald Trump ya sake tsallake wani harin bindiga inda aka yi ta harbe-harbe a kusa da shi a wani yanki na Jihar Florida, a ranar Lahadi.

Kakakinsa, Steven Cheung, ya ce Trump ya na cikin ƙoshin lafiya inda ya ce su na aiki da hukumomi wajen gano ainihin bayanan al’amarin.

Kawo yanzu babu tabbatcin harin an kai shi ne musamman don Trump kamar yadda kakakin nasa ya wallafa a shafin X.

Hakan na zuwa ne watanni biyu bayan wani harin kisa da aka kai wa tsohon shugaban a lokacin yawon neman zaɓe a yankin Pennsylvania.

An kuma sanar da Shugaban ƙasar, Joe Biden da Mataimakiyarsa Kamala Harris kan cewa babu abin da ya samu Trump.

By Babaji