Har yanzu akwai marubutan da ba su rungumi sauyin da zamani ya kawo ba – Haiman Raees 

Spread the love

Ina da kyakkyawan zato game da adabin Hausa a nan gaba

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Jamilu Abdulrahman, wanda aka fi sani da Haiman Raees ba baƙo ba ne a tsakanin marubutan onlayin, musamman ma masu hulɗa da mahajojin kamfanin Bakandamiya Hikaya, inda bayan kasancewarsa marubuci kuma manazarci, harwayau shi ne yake jagorantar ɓangaren Bakandamiya Reading Club (BRC) sashin da ke kula da ilimantar da marubuta da inganta alaƙarsu da masu karatu. Haiman, wanda masanin harshen Indiyanci ne da Turanci, ya yi rubuce-rubuce a ɓangarorin adabi daban-daban. Bayan kasancewarsa marubucin waƙoƙin Hausa da Turanci, yana kuma nazari kan fasahohin waƙoƙin Indiya, marubucin wasan kwaikwayo ne kuma jarumi, malamin makaranta ne kuma ɗanjarida. A tattaunawarsa da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, Haiman ya bayyana takaicinsa na yadda har yanzu wasu marubuta suke ɗari-ɗari da rungumar sabuwar fasahar zamani da sauye-sauyen da ake shigo da su don inganta rubutun adabi. Ga yadda hirar tasu ta kasance. 

MANHAJA: Ko za ka iya gabatar da kanka? 

HAIMAN: Assalamu alaikum. Sunana Jamilu Abdulrahman, amma an fi sani na da Haiman Raees. Na yi harkoki da dama kuma gashi yanzu ina yin wasu, kuma in Allah ya ba mu aron rai zan yi wasu a gaba. 

Daga cikin harkokin yau da kullum da na yi akwai fassarar finafinan Indiya da na Amurka zuwa harshen Hausa. Sannan na yi aikin gidan rediyo na ɗan wani lokaci da Alheri Radio Kaduna, Kada FM Kaduna da kuma ɓision FM Kaduna duka a ƙarƙashin harkokin finafinai da waƙoƙin Indiya. Na yi harkar koyarwa a makarantu masu zaman kansu har guda 6. Sannan na yi harkar waƙa, kuma na samu horo game da yadda ake fitowa a finafinai, a wannan lokaci ne har na samu wani laƙabi na ‘the obedient artiste.’ Na yi sana’ar gidan burodi, na yi sana’ar hatsi kuma na yi harkar agaji na JIBWIS. 

Za mu so mu ji tarihin rayuwarka, da gwagwarmayar da ka sha ta karatu.

An haife ni a ranar uku ga watan Maris shekara ta 1993 a garin Gadar Gayan, wanda ke gundumar Fanshanu, ƙaramar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna. Na fara karatuna na boko da kuma na addini duk a garin Gadar Gayan kafin daga baya na koma cikin garin Kaduna inda na cigaba, kuma har yanzu dai ina cigaba da karatu. Ina da aure kuma yanzu haka ina zaune ne a cikin garin Malalin Gabas da ke Kaduna. Baya ga haka, ni marubuci ne, manazarci, kuma mai sharhin littattafai da finafinai tare kuma da fassarar waƙoƙin finafinan Indiya. Har yanzu ina cigaba da karatu ne. 

Me ya sa ake kiran ka da Haiman Raees, a maimakon sunanka na asali?

Haiman inkiya ta ce tun ina firamare, kuma na samo shi ne daga cikin littafin Gwagwarmaya na Shehu Usman Muhammad wanda yake cigaban littafin Mazan Fama ne. Daga baya Raees ɗin ya samu sakamakon shugabanci.

Mene ne yake baka sha’awa a harkar adabi, kuma wanne ɓangare ka fi ƙwarewa?

 Komai da ya shafi adabi yana burge ni kuma yana ba ni sha’awa. Amma na fi shajja’a idan na ga an yi nagartaccen aiki a kowanne ɓangare na adabin. Gaskiya zan iya cewa kusan kowanne ɓangare ana damawa da ni. Domin shukran la faharan, na iya rubuta waƙa kuma na iya rera ta, na iya rubuta wasan kwaikwayo kuma na iya wasan kwaikwayon, na iya rubuta labaran zube kuma na iya karanta su. Ka ga kuwa sai dai in ce, Alhamdulillahi. 

Ka rubuta littattafai guda nawa? Kawo mana sunayensu da bitar 3 daga cikinsu.

 Zuwa yanzu na rubuta littattafai guda goma sha biyu. Da suka haɗa da na Hausa da kuma na Turanci. Littattafan su ne, ‘Fasaha Haimaniyya’, ‘Fatalwar Sinu’, ‘Birnin Sahara’, ‘ɓoice Of Loɓe’, ‘Ba’indiya’, ‘Malam Jatau’, ‘Baƙar ƙaddara’, ‘Warwara’, ‘Falsafa’, ‘Tambaya’, ‘Mysterious Pen’, ‘Muryar Dalili’.

Amma littafin ‘Falsafa’ da ‘Mysterious Pen’ ba ni kaɗai na rubuta su ba, haɗaka ce muka yi ni da Mujahid Nuhu Yusuf (Matashi), kuma dukkansu littattafan rubutattun waƙoƙi ne. 

Shi dai littafin ‘Birnin shahara’ labari ne na wani matashi mai suna Haidar, ba tare da ya san ya aka yi ba kawai sai farkawa ya yi ya tsinci kansa a wani ɓoyayyen babban birni a cikin Sahara wanda babu mai iya shiga cikin wannan gari ko fita face ya kasance ɗan asalin garin, ko ganin birnin ma ba a iya yi saboda an tsafance shi. Labarin ya taɓo abubuwa da dama da suka shafi soyayya, addini, tarihi da tsafi, musamman cinikin bayi da kuma al’adu. Littafin shi ne tubalin ginin labaran DLH (wato Duniyar Labaran Haiman) don haka ina matuƙar ji da shi. 

Shi kuma littafin Malam Jatau rubutaccen wasan kwaikwayo ne, wanda yake ɗauke da labarin wani mutumin ƙauye baduniyi, mai mata uku da yara da yawa. Cakwakiyar da ake tafkawa a gidan nan nasa ba a magana. Labari ne da ya taɓo yanayin zamantakewar iyali da raha da kuma nishaɗi. 

Littafin ‘Baƙar ƙaddara’ kuwa, littafi ne na gajerun labarai. Kowanne labari da muhallinsa, da kuma irin ƙalubalen da jaruman ciki suka fuskanta, amma duka suna ba da misalan irin munanan ƙaddarori ke faɗa wa ‘yan’adam ba tare da sun yi aune ba. Littafi ne mai taɓa zuciya sosai, domin komai juriyar mutum da wuya a ce duk cikin labaran babu wanda ya taɓa masa zuciya, domin an kawo misalai ne irin wanda mutane za su iya alaƙantuwa da su a ciki.

Kamar sauran litattafan da ke ƙarƙashin DLH, dukka waɗannan labaran suna da alaƙa da juna. Wasu alaƙa ta kusa, wasu kuma ta nesa, wasu ma alaƙar da ke tsakaninsu ba za ta bayyana a yanzu ba sai nan gaba idan wasu litattafan nawa suka fito. In Sha Allah.

Mene ne DLH ke nufi? Kundin labarai ne ko kuma wata taska ce ta rubutu?

Hikimar da ke cikin ƙirƙiro DLH na da yawa kuma ba ta da iyaka. Da farko dai, duk labarai ko waƙoƙin da nake rubuta wa da suke fitowa a ƙarƙashin DLH gabaɗaya suna faruwa ne a wata duniyar ta daban mai kama da tamu duniyar. A farkon kowane littafi ina yin wannan bayanin, da haka na kauce wa matsalar kada wani ya yi tunanin labarinsa rayuwarsa na ɗauka ko wani abu makamancin haka. Sannan, tun da labaran a duniya ɗaya suke faruwa, to akwai yiwuwar mutane, wurare, abubuwa da ma kusan komai na kowanne labari ya cakuɗu da wani labarin ko kuma su haɗu. A taƙaice dai na yi amfani da salon ɗin ‘multiɓerse’ ne wajen ƙirƙiro ‘in-book uniɓerse’ na Hausa domin samar da mabanbantan labarai masu alaƙa da juna ta fuskoki da dama. Kuma tunda a wata duniyar labaran ke faruwa, to babu irin canji ko sauyin da ba zan iya yi musu ba. Ka ga kenan na samar wa da kaina wani ‘yanci na rubutu wanda babu wani abu da zai katange ni daga yin kowanne irin rubutu nake son yi.

Mene ne alaƙarka da kamfanin Bakandamiya?

Ni marubuci ne kuma edita a kamfanin Bakandamiya. Amma abu mafi muhimmanci shi ne, ni masoyin Bakandamiya ne na gaskiya da gaskiya. Abin da ya sa nake son kamfanin kuwa shi ne, saboda na fahimce su sosai kuma na yi imani da manufarsu ɗari-bisa-ɗari. Wannan ya sa dukkan wani aiki da na yi na adabi a can kawai nake ɗorawa saboda ba da tawa gudunmuwata wajen ganin cigaban kamfanin. To, amma ka fahimta, ba wai ido rufe kawai nake yi musu wa kamfanin irin wannan soyayya ba. Marubuta da dama suna ɗora ayyukansu a shafukan turawa inda suke ɗan samun abin masarufi, to me zai hana mu goyi bayan namu? Idan ba ma haka mu ɗin ta yaya za mu miƙe?

Akwai harkoki da dama da kamfanin ke gudanarwa da suka shafi adabi da kasuwanci, wanda kuma al’ummarmu za ta amfana da su sosai ko kuma in ce suna kan amfana. Daga ciki akwai irin su Hikaya, wanda shafi ne da suka buɗe domin marubuta da masu karatu. Marubuta na iya ɗora littattafansu na kuɗi ko na kyauta. Masu karatu kuma na iya shiga su karanta na kyauta kuma suna iya yin subscription domin karanta na kuɗi. Sannan akwai muƙaloli da ake ɗorawa a shafin waɗanda za su taimaka wajen ilimantar da marubuta sosai. 

Akwai kuma tsarin Bakandamiya Encyclopedia, wanda shi kuma shafi ne da aka tanada domin samar wa al’umma da bayanan ƙwararru da suka shafi lafiya, kimiyya, fasaha da sauran fannoni masu yawa a cikin harshen Hausa.

Sai tsarin Bakandamiya Kitchen. Shi kuma shafi ne da suka tanada domin samar wa da iyaye mata sirrukan girki na zamani da yadda ake yinsu.

Harwayau, a ƙarƙashin ita Bakandamiya ɗin akwai wani shafi da aka sa wa suna Tambayoyi. Shi kuma shafi ne da suka tanadar domin jama’a su riƙa yin tambayoyi, ana samun masu ba da amsa a tsakanin masu karatu, domin ƙaruwa da juna.

Sannan sun ƙirƙiro da Bakandamiya ɓitals, wanda shi kuma shafi ne da suka samar domin faɗakarwa a kan harkokin kiwon lafiya. Ga juma shafin Bakandamiya Shopping. Shi kuma shafi ne da suka tanada domin yin siyayya ta onlayin, kuma suna tura wa mutane kayan da suka saya zuwa kowacce jiha a faɗin Nijeriya.

Suna ma kuma da tsarin ba da tallafin karatu na Annual Scholarship, wanda ke samar da damarmakin yin karatu kyauta ga ɗaliban da suka cancanta a ɓangarori dama a cikin gida Nijeriya da kuma ƙasashen waje.

Kaɗan kenan daga cikin ayyukan da suke gudanarwa, kuma dukkan waɗannan shafuka sun samar musu da manhaja wadda kowa na iya saukewa daga Google Playstore ya amfana da su.

A bisa wannan dalili, ba na tunanin duk wani mai kishin al’ummar Hausa da Hausawa zai gaza nuna musu irin ƙaunar da nake nuna musu, domin wannan ba ƙaramin cigaba ba ne ya zo mana, don da haka ne mu ma za mu shiga cikin takwarorinmu a fafata da mu.

Wacce riba marubuta suke samu ta hanyar ɗora littattafansu a manhajar Bakandamiya Hikaya?

Akwai riba sosai gaskiya. Na farko dai akwai awalaja kuɗi kenan. Na biyu akwai samun damar tafiya tare da zamani. Sannan akwai samun damar cuɗanya da wasu marubutan. Akwai kuma bangon littafi da Hikaya ke yi kyauta wa dukkan marubutan da suka ɗora littattafansu da dai sauran abubuwa.

Wacce gudunmawa ka ke bayarwa a Bakandamiya Reading Club?

Ni ne jagoran BRC. A shekarar da ta gabata ne kafamfanin Bakandamiya suka danƙa min ragamar jagorantar wannan zaure tare da sauran abokan aikina. Bayan mun cika shekara guda kuma sai aka sake tabbatar min da muƙamin nawa, wanda har yanzu nake kai kuma ina bakin ƙoƙarina. 

Ko za ka gaya mana manufar kafa wannan zaure na BRC da ayyukan da ku ke gabatarwa?

Manufar zauren BRC shi ne jawo hankulan mutane domin su zo mu ƙaru da juna ta hanyar musayar basira da ilimi. Aƙalla muna da manya-manyan shirye-shiryen da muke gudanarwa. Daga ciki akwai sharhin littattafai, wanda muke zaƙulo littafi tare da gayyato wani masani domin ya zo ya yi sharhin wannan littafi domin jama’a su ƙaru. Akwai shirin Kaifin Alƙalami, shi wannan shiri ne da kan gayyato masana a fannin rubutu su zo su gabatar mana da maƙala akan wani batu da ya shafi harkar rubutu. Akwai kuma Tattaunawa ta Musamman wato Special Presentations da muke gabatarwa, wanda mu kan gayyato mutane daban-daban su zo su yi mana bayani ko ƙarin haske game da abubuwan da suka shafi rayuwar yau da kullum domin amfanin jama’a. A taƙaice dai, so muke mu ƙara wa jama’a ƙaimi wajen dagewa game da ilimi ta hanyar rubutu da karatu. 

Waɗanne ƙalubale ku ke fuskanta a BRC wanda ku ke ganin marubuta da masu karatu za su iya ba da gudunmawa wajen inganta su?

Babban ƙalubalen da mu ke fuskanta a BRC shi ne ƙarancin goyon baya daga jama’a. ƙoda yake Alhamdulillahi yanzu an fara fahimtar inda muka dosa, amma duk da haka muna buƙatar goyon baya domin cimma ƙudurin zauren. Da a ce mambobinmu za su samun zarafi a duk lokacin da mu ke gabatar da shirye-shiryen BRC suna shiga ana yi tare da su, to tabbas da shirye-shiryen sai sun fi armashi. Domin wani na iya yin tambayar da za ta sa a yi bayanin da wasu za su ƙaru ta hanyar da mu kammu ba mu sani ba. 

Wanne sauyi wannan tsarin na Bakandamiya Reading Club ya kawo a duniyar ilimi da rubutu?

Babban sauyin da BRC ya kawo shi ne kaucewa daga irin tsarin da aka saba da shi na dandalin marubuta musamman a tsakanin marubuta littattafan Hausa. Da farko dai ba mu ɗauki Hausa kaɗai a matsayin harshen gudanar da ayyukan BRC ba. Sannan ba mu taƙaita kanmu ga sharhin littafi kawai ba, a’a, har ma da tattaunawa game da wasu muhimman abubuwa da suka shafi rayuwar al’umma. To, kuma duk da haka muna saka gasa domin zaburar da masu karatu da marubuta su ƙara dagewa a kan harkar ilimi. Gayyato masana a fannonin da suka dace domin su zo su fayyace mana abubuwan da suka kamata game da batutuwan da muke sa wa na daga cikin abubuwan da mambobinmu suke amfana da su. 

Bayan shekara guda da BRC ta yi, kana ganin alamun kwalliya tana biyan kuɗin sabulu?

Tabbas akwai alamun hakan, domin mutane sun fara fahimtar inda muka nufa, kuma in sha Allah muna sa ran za su ba mu gudunmuwa a gaba fiye da yanzu. Ka ga a cikin shekara guda ɗin nan, a zauren Facebook kawai muna da mabiya sama da dubu huɗu. Ka ga kuwa samun mabiya sabon abu irin haka a ɗan ƙanƙanin lokaci babbar alama ce ta yiwuwar samun nasara a gaba in sha Allah. 

Kun gudanar da bikin cika shekara guda da buɗe zauren Bakandamiya Reading Club, waɗanne abubuwa ku ka gudanar yayin bikin?

Mun gudanar da abubuwa sosai gaskiya. Da fari dai mun yi taƙaitacciyar bita game manufar kafa BRC, sannan mun bai wa ƙungiyoyin da suka taka muhimmiyar rawa a gasar BRC tare da wata ƴar awalaja da kuma shaidar girmamawa da wasu ‘yan littattafai. Wannan a taƙaice kenan. 

Yaya ka ke hangen harkar adabin Hausa nan da wasu shekaru masu zuwa?

Haƙiƙa ina da kyakkyawan zato game da adabin Hausa a nan gaba, domin a bisa yadda abubuwa suke tafiya, matuƙar aka saki jiki kuma aka karɓi irin sauye-sauyen da zamani ke kawowa, to nan da shekaru 15 zuwa 20 adabin Hausa na iya kai wa matakin da ba a yi tsammani ba. Dalilin da ya sa na ce haka kuwa shi ne, ka cire jiga-jigan malaman Hausa da masana adabi da muke da su ziryan a ƙasar nan, ka kuma cire ɗimbin ɗaliban da ke karantar harshen Hausa, waɗanda wasu ma asalin su ba Hausawa ba ne, ka kuma cire irin yadda Hausa ta gawurta a duniya, yanzu kuma wani sabon ƙarfi ne harshen ke samu wanda zai ƙara haɓaka adabin tare da tunkuɗa shi zuwa mataki na gaba. Wannan ƙarfi kuwa shi ne, yanzu ba sai ɗaliban da suka karanci Hausa kawai suke yin rubutu da harshen ba. Masana daga fannonin ilimi da dama yanzu suna rubutu a fagen da suka ƙware domin mutane su amfana. Ga shi ana ta ƙara samun ƙwararru da ke fassara ayyukan da aka yi daga wasu harsuna zuwa Hausa, ga shi kuma yanzu an fara samun matasa masu hazaƙa da kishi suna ƙara shiga cikin harkar adabin. To, ka ga wannan ba ƙaramin al’amari ba ne. Kwanakin baya har talla na gani ana neman ma’aikata da za su yi wa wani kamfani aiki wajen gina Artificial Intelligence da harshen Hausa. To, in kuwa har tafiyar nan ta ci gaba a haka, tabbas kwalliya za ta biya kuɗin sabulu. 

Shin a nazarin da ka yi kawo yanzu kana ganin marubutan adabi suna da saurin rungumar sabbin hanyoyi na zamani irin naku?

Gaskiya ba su da shi. Domin da yawan marubuta a yanzu sun fi son bin hanya mai sauƙi ne kawai domin su samu wani abu nan da nan, amma ba su damu da kimar wannan rubutun nasu da abin da zai biyo baya a shekaru masu zuwa ba. Alal misali, a sashen Hikaya wanda kamfanin Bakandamiya ta ware domin marubuta da masu karatu, ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da suka bambanta Hikaya da sauran shafuka shi ne, su kan ware lokaci da komai nasu domin inganta rubutun marubuta, saɓanin wasu kafofin da duk yadda marubuci ya saka littafi haka kawai za su sake shi. To, su kuma marubutan sau da dama ba sa son irin wannan gyara ko ingantawa da za a yi wa aikin nasu saboda wasu ra’ayoyi nasu. Kuma duniya cigaba take yi, sannan komai ba ya tafiya sai da tsari mai kyau. Wani abu kuma mai cin rai shi ne, da yawan marubutan onlayin kawai sun ɗauki shafuka irin na Hikaya tamkar soshiyal midiya, komai suka ɗauka sai su watsa kawai kuma su kira shi littafi. To, in ka haɗa masu yin irin haka da masu gudun irin sabbin cigaba da zamani ke kawowa sai ka ga mutanenmu na daƙile kansu daga samun nasara mai yawa a harkar rubutu, saɓanin takwarorinsu. 

Mene ne yake baka sha’awa a waƙoƙin Indiya?

Abubuwan suna da yawa. Na farko akwai yare, na fi sha’awar Hindi fiye da sauran yarukan ƙasar Indiya, domin shi na fi ji. Kuma sun iya jera kalamai cikin hikima, tare da tsara zance. 

Tsakanin ƙwallon ƙafa, kallon fim, da hira a zaurukan sada zumunta, wanne ya fi cinye maka lokaci?

Karatu ya fi komai cinye min lokaci. Daga shi sai kallon fim. Kuma kallon ina yi ne da gaske kamar yadda nake karatu. Ba na yarda na tashi ban ƙaru da komai ba. Don ƙwallon ƙafa kuwa, in don ta ni ne ba ma za a yi ta ba. 

Ban da harkar adabi wanne abu ne ya fi ɗaukar hankalinka?

To, gaskiya dukkan abubuwan da suka fi ɗaukar hankalina suna da alaƙa da adabi, amma cututtuka da magunguna ma suna taka irin tasu rawar, saboda mahaifina masanin magungunan gargajiya ne sosai, kafin Allah Ya yi masa rasuwa. 

 Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarka?

Gaskiya suna da yawa. Daga cikin na Hausa dai akwai ‘ƙudan da ba shi da mafaɗi, shi ke bin gawa har kabari’. daga cikin na Turanci kuma akwai ‘We can only be who we are, nothing more and nothing less.’

Masha Allah. Na gode ƙwarai da gaske.

 Ni ma na gode da samun wannan dama.

By ukarofi