Na hannun daman tsohon gwamnan Legas Jakande ya samu karramawa ta DRTS a Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Mai taimaka wa marigayi tsohon gwamnan jihar Legas (Dakta Lateef Kayode Jakande), Kwamared Salihu Ɗantata Mahmud ya shiga sahun waɗanda suka samu lambar yabo daga ɓangaren wasanni na ofishin hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa DRTS.

Mista Andrew Agbasi shi ne shugaban reshen wasannin inda Daraktan hukumar, Dakta Abdullateef Bello shi ya gabatar da kyautukan lambobin yabon inda ya yaba wa Salihu kan taimakonsa ga ofishin wajen ƙarfafa alaƙa da ke tsakanin ɓangaren da ofishin labarai.

Ya yi kira gare shi da ya faɗaɗa taimakonsa na wasanni zuwa sabon tsarin aiki na kwana uku da jami’an hukumar ke yi a hanyoyin Abuja waɗanda suka zama Litinin, Laraba da Juma’a kaɗai.

Kwamared Salihu shi ne tsohon mai taimakawa musamman ga harkokin Arewa, babban jami’in ‘Daily News’, tsohon Sakataren Labarai, Sakatare na Ƙasa kuma tsohon Manajan kamfanin rukunin gidajen Good Homes reshen Arewa wanda mallakar marigayi Lateef Jakande ne.

Kazalika, Salihu ya yi godiya ga shugaban ɓangaren wasanni tare da sadaukar da lambar yabon nasa ga Ministan Abuja, Nyesom Wike da Darkatan hukumar.

Taron ya samu halartar manyan masu alfarma da suka hidimta wa al’ummar ƙasa.

By Babaji