An fara ƙirga ƙuri’u bayan INEC ta ƙara lokacin zaɓe a wasu yankuna a Edo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Bayan watanni ana yawon neman zaɓen kujerar gwamnan Jihar Edo, a yau ne a ke kaɗai kuri’a don sauya gwamanti mai ci kasancewar wa’adinta ya zo ƙarshe.

Jam’iyyu 17 ne hukumar zaɓe, INEC ta tantance waɗanda ke gwabzawa a zaɓen don karɓar ragamar mulkin daga hannun gwamna Godwin Obaseki wanda wa’adinsa zai ƙare a watan Nuwamba.

Ɗan takara Asue Ighodalo na jam’iyyar PDP da Monday Okpebholo na APC da kuma Olumide Akpata na LP su ne manyan ƴan takarar kujerar.

A na gudanar da zaɓen ne a mazaɓu 4,519 a ƙananan hukumomi 18 na jihar.

Tsohon shugaban Hukumar Kula da Ƴancin Ɗan-adam (NHRC), Chidi Odinkalu ya yi gargaɗin cewa matuƙar INEC ta yi wasa da zaɓen, Nijeriya ka iya fuskantar wasu matsaloli.

Tuni dai jami’an tsaro da na INEC suka cigaba da gudanar da ayyukansu don ganin an kammala zaɓen cikin lumana da kwanciyar hankali.

By Babaji