Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Gobe Asabar, 21 ga Watan Satumba, al’ummar duniya za ta yi bikin Ranar Zaman Lafiya ta Duniya na wannan shekara, 2024. Kuma kamar yadda duk shekara aka saba, ana sa ran gudanar da taruka daban-daban, wanda masu ruwa da tsaki kan harkokin shugabanci da ba da gudunmawa kan zaman lafiya da sasanta rikice-rikice za su gudanar. Sannan akwai tattaunawa da manema labarai, tattakin wayar da kan jama’a, da kuma ganawa da magabata game da rawar da za su iya takawa a hukumance wajen ƙara inganta zaman lafiya da tsaro a yankunansu.
A bana, taron yana son mayar da hankali ne kan yadda za a haɗa hannu wajen ganin an yaƙi gurɓacewar muhalli, da rashin wadatar abinci, da kuma samar da tsaftataccen ruwan sha ga jama’a musamman a wuraren da ake fuskantar ƙarancin ruwan sha da kuma fari. Duk da kasancewar yanzu lokaci ne na damina, kuma akasarin jihohin ƙasar nan sun samu albarkar saukar ruwan sama, manoma da dama, a inda ake da sauƙin matsalar tsaro, sun duƙufa wajen noma domin samar da wadatar abinci, wanda za a ajiye a gida don yau da gobe, da kuma wanda za a fitar kasuwa don samun na cefane.
Sai dai wani yana iya tambayar cewa, me ya haɗa batun zaman lafiya da noman abinci? Babu shakka duk wani abu na rayuwa yana da alaƙa da zaman lafiya, domin idan mun yi tunani za mu gane cewa, shi fa zaman lafiya ba kawai yana nufin rashin faɗa ko rashin rikici ba ne, yana nuni ne da yanayin da mutum ke zaune cikin kwanciyar hankali, ba tare da wata fargaba ko tsoron wani abu zai iya katse masa jin daɗi da walwala ba. Duk abin da zai sa mutum cikin ƙunci da damuwa to, ya shafi walwalarsa da zaman lafiyarsa. Shi kuma zaman lafiya ba ya inganta sai akwai natsuwa, kwanciyar hankali, tsaro da cigaba.
Wani masanin harkokin zaman lafiya da sasanta tsakanin al’umma, Carl Juntung, ya bayyana wasu rabe-rabe na abubuwan da suka shafi zaman lafiya, inda ya ke nuni da cewa, akwai zaman lafiya kashi uku. Zaman lafiya irin na zaman doya da manja, wanda ke nuna ana zaune tare, babu faɗa, babu kashe-kashe da ƙone-ƙone, amma kuma kullum ana zaune cikin fargaba da tsoro, babu yarda da juna. Akwai zaman lafiya mai ma’ana, wanda ake zaune tare cikin girmamawa da yarda da juna, da kiyaye haƙƙoƙin jama’a, rashin nuna wariya ko ƙyama. Sai kuma zaman lafiya mai ɗorewa, wanda ake gina shi a kan ginshiƙin adalci, da daidaito, da kula da haƙƙin kowa, inda zai zama ba a bar wata ƙofa da za ta nuna akwai rashin yarda ko ƙorafi na rashin bai wa wani ɓangare dama fiye da wani ɓangare ba.
Ashe kenan idan muka lura da kyau za mu fahimci cewa, a yadda yanzu duniya ke cike da matsaloli iri-iri, babu wani ingantaccen zaman lafiya da ake samu, sai dai a ce ana zaman doya da manja. Saboda halin rashin tsaro da ake samu a wasu yankuna, kama daga yaƙe-yaƙe da manyan makamai, rigingimu na ƴanta’adda, ’yan bindiga, da masu tada ƙayar baya. Rikicin manoma da makiyaya, rikicin ƙungiyoyin matasa masu shaye-shaye da amfani da makamai wajen aikata laifuka, matsalar fari da zaizayewar ƙasa, da kuma matsalar da ta zama gidan kowa da akwai, ta yunwa da talauci.
Waɗannan duk matsaloli ne na rayuwa da suke hana wa ɗan adam rashin kwanciyar hankali da ƙalubale kan yadda zai yiwu ya samu sauƙin rayuwa. Majalisar ɗinkin Duniya na ganin akwai buƙatar al’ummar duniya su haɗa hannu don ganin an ba da gudunmawa ta kowanne ɓangare, domin samar wa ɗan adam kyakkyawar rayuwa. Saboda akasari wasu matsalolin ɗan adam ne da kansa yake jawo su ta hanyar wasu ayyuka da yake gudanarwa masu kawo saɓani tsakaninsa da abokan zamansa, ko muhallinsa.
Zamantakewar ɗan adam da muhallinsa abu ne da yake ɗaukar hankalin duniya a halin yanzu, sakamakon yadda ɗumanar yanayi, gurɓacewar muhalli, fari, janyewar koguna, tsanantar zafin rana, da yawan samun ambaliya ke barazana ga cigaban tattalin arziƙi da walwalar al’umma. Babu ma kamar yadda ake samun komabaya a harkar noma da kiwo. Mun ga yadda tsananin zafin rana da fari ya haifar da rashin noma da bushewar ƙasa a wasu wurare, inda a dalilin haka mutane da dama suka shiga yunwa, yaransu kuma suka kamu da cutar tamowa da ke sanya tsananin rama da ƙanjamewar jiki.
Ko a kwanakin baya mun ga yadda ibtila’in ambaliya ya afkawa wasu jihohin ƙasar nan, musamman ma dai Jihar Borno, inda ɓallewar madatsar ruwa ta nutsar da dubbanin al’ummar garin Maiduguri cikin ruwa, wanda haka ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi masu yawan gaske. Duk da kasancewar an danganta abin da ya faru kan sakacin hukumomi da rashin ɗaukar shawarar ƙwararru. Amma za mu iya cewa wannan bala’in ambaliya na daga cikin mafi munin ibtila’i da ya faru da wata al’umma a ƙasar nan, a shekarun baya-bayan nan. Bayan masifun ta’addanci da rashin tsaro da yankin ya fuskanta a baya, da wanda yankin arewa maso yamma yake kan fuskanta a halin yanzu.
Zaman lafiya ta fuskar tattalin arziki abu ne mai matuƙar muhimmanci, wanda yanzu babu abin da al’ummar ƙasar nan ke tsananin buƙata kamar samun abinci a farashi mai rahusa, samun kuɗaɗe da za a iya amfani da su wajen biyan buƙatun rayuwa, ƙarin albashi mai tsoka, sassauta farashin man fetur, da tsaro kan rayuwar su. Yadda jama’a da dama ke wuni da kwana cikin yunwa, yara ke zaune a gida babu damar komawa makaranta, saboda rashin kuɗin makaranta, karyewar jarin masu ƙananan sana’o’i, ƙaruwar yawaitar mutuwar aure, yawan shigar matasa harkar shaye-shaye da faɗace-faɗace, abin tashin hankali ne ainun. Rayuwar ƙunci da ma’aikata masu karɓar ƙaramin albashi suke fuskanta su da iyalansu, abin a tausaya ne matuƙa. An kai wani hali na, innalillahi wa inna ilaihir raji’un!
Don haka bikin Ranar Zaman Lafiya ta Duniya na bana yana da abubuwan tattaunawa da dama da suka shafi yadda rayuwa take kasancewa a halin yanzu. Da buƙatar da ake da ita a wajen hukumomi su tashe tsaye su yi da gaske wajen daƙile abubuwan da ke kawo wa ’yan Nijeriya cikas wajen gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da lumana.
Sannan kamar yadda na faɗa a makon da ya gabata lallai ne a jinjinawa ƙungiyoyin sakai masu aikin zaman lafiya da sasantawa, da ke aiki ba dare ba rana, domin samar da shawarwari da gudunmawa kan yadda jama’a za su fahimci muhimmancin zaman lafiya. Tare da taimakawa hukumomin gwamnati da ake ɗorawa nauyin sasanta ɓangarorin al’umma da masu faɗa a ji don a samu cigaban tsaro da zaman tare, cikin lumana da kwanciyar hankali. Idan al’ummar duniya ta rungumi wannan gangami na tabbatar da zaman lafiya a kowanne mataki na rayuwa to, babu shakka duniya za ta yi daɗin zama, kuma ayyukan cigaba za su yalwata, arziƙin mu zai dawo da daraja da martaba.
Allah Ya bamu zaman lafiya bakiɗaya. Amin.
