Ina son na samu haihuwa – Bobrisky

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Shahararren ɗan daudu, Idris Okuneye, wanda aka fi sani da Bobrisky, ya bayyana sha’awarsa ta samun ‘ya’ya na kansa.

Bobrisky ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da mai shirin Egungun of Lagos.

A tattaunawar, Egungun, ya tambaye ɗan daudun ko ina yake hango kansa a shekaru biyar masu zuwa?

Bobrisky ya ba shi amsa da cewa, “Ina hangen kaina a shekaru biyar masu zuwa tare da kyawawan ‘ya’yana.”

ɗan daudun ya kuma ƙara da bayyana irin kuɗaɗen da ya kashe wurin yin aikin ƙarin mazaunai.

“Na kashe kusan miliyan shida wurin aikin ƙara min girman mazauni.”

By ukarofi