Daga AISHA ASAS
Sau da yawa shaiɗan ke ƙawata mana abu ya nuna mana zai iya haifar mana ɗa mai ido, wani lokacin ya sanar da mu shi a matsayin hanya ƙwaya ɗaya da za ta iya fitar da mu daga halin da muke ciki. Tare da ba mu tabbacin ba wanda zai sani, ko ba abinda zai faru, duk da cewa wani ɓangaren na zuciyarmu na sanar da mu illar da ke tattare da abinda muke shirin aikata wa.
Finafinan batsa ko rubuta batsa ba ɗabi’a ce da ke da gindin zama a kowanne addini da ke kewaye da ƙasashen Afirka ba. Haka a nan kurkusa ban ga wata al’ada da ke nuni da ka siyar da jikinka ga duniya ba ta hanyar yin wasan kwaikwayo na batsa don kallon mutane ba. Wanda kuwa a kullum aikata shi yake da nadama daga baya, ba wai a iya mu Afrika da addinai da al’adunmu ba su koyar da mu ba, har ga su karan kansu Turawan da suka ƙirƙiro shi.
Wannan ce ta kasance ga ɗaya daga cikin jaruman batsa, wanda ya bayyana harkar a matsayin hanyar da ba uwa ba riba.
Jarumin finafinan batsa na ƙasar Cameron wanda aka fi sani da Ze Gladiator, ya bayyana takaicinsa kan harkar da yake yi, inda ya bayyana ya daina fim ɗin batsa sakamakon yadda ba ta haifar masa ɗa mai ido ba, maimakon haka, ya bayyana cewa, kamfanin da yake yi wa aiki na amfani da shi wurin gina kansu kawai.
“A yau ina mai nuna nadamata ta zama jarumi a D0rcel Afrika. Magana ta gaskiya tun a farko na fara ne sakamakon matsin rayuwa, ba ni da aiki, kuma a matsayina na uba, wanda yake tare da uwar ‘ya’yana, ba ni da abinda zan kawo na buƙatun yau da kullum. Wannan ne dalilin da ya sa na faɗa wannan harka don samun na buƙatuna da iyalina, kuma da fitowa har bakwai ne na samu kuɗina na farko, wato CFA 150,000, ” cewar Ze Gladiator.
Ya ƙara da cewa, “A yadda suka bayyana, ba wanda zai san ina wannan harkar, domin ba za su siyar da fim ɗin a nan ba, maimakon haka suna siyar da su ne a ƙasashen waje.
A ɓangare ɗaya, matata wadda ta san halin da muke ciki ta fara zargin inda nake samo kuɗi, har ya kasance ta fara tambaya ta. Hankalina kwance na mata ƙarya, saidai ramin ƙarya ƙurare ne, domin ba jimawa sosai, a wata rana mahaifiyata ta kira daga ƙauye, ta ke sanar da ni an turo mata wani faifan bidiyo da ya haska ni tare da mace.
Wannan ne yadda dukka ahalina suka san abinda nake yi. Don haka sai na sake na cire tsoro na ci gaba da abinda nake yi. Saidai duk da hakan ban iya shiga mutane sosai kamar baya.
Babban ƙalubalen kuwa shi ne, kowa tunanin yake ina samun miliyoyi a wannan harkar, duba da irin tarin dukiyar da masu irin wannan aikin ke samu a wasu ƙasashe. Saidai abinda ba su sani ba, shi baƙin mutum zalamarsa ta yi yawa, komai nasu, masu aiki kuwa komai babu.
Abinda zai ƙara saka nadamar shiga wannan harkar kai dai a fuskar abinda ake gani yanayin aikin da muke yi kuwa shi ne, ba wani jarumi a cikinmu da yake da kwangilar aiki da kamfanin, kuma ba wanda yake da wani tanadi na kula da lafiyarsa kamar yadda ake yi wa masu irin wannan aikin.
Idan ciwo ya samu jarumi a wannan harkar, to suna ƙyale shi ne ya je ya ƙarata, ga shi ba wata kulawar da za ta hana kamuwa da cututa. Ni kaina na taki sa’a ne da na fice ba tare da guzurin wata cuta ba.”
Jarumin ya ƙara da kira ga jama’ar Kamaron da su daina yi masa kallon wanda ya samu arziki da dacewa sakamakon wannan aiki, inda yake cewa, “Ina kira ga mutanen Kamaroon da su daina yi min kallon wanda ya samu arziki ta sanadiyyar D0rcel, domin duk wannan aikin da nake yi, bai zama silar arzikina ba, domin ina aikin koyar da motsa jiki tun daga ƙarfe shida na safe har shida na yamma a kowacce rana.
Don haka labarin fim ɗin batsa ya ba ni komai na rayuwa duk ƙanzon kurege ne.”
