Wannan ba sabon abu ba ne, daɗaɗɗen al’amari ne da ya shafe sama da shekaru 64 da shiryawa, wanda ya faro daga samar da wasu gurɓatattun mutane da aka ɗauke su haya don lalata Arewacin Nijeriya, ta hanyar ƙirƙirar ‘yan ta’adda masu da’awar musulunci da sunan jihadi, da waɗanda suke da’awar kafa yankinsu da sunan ƙasa. Na sha faɗa kuma ina ƙara faɗa, da yawan matasanmu ba su san wannan al’amari ba, kuma waɗanda suka sani ba su da kishi a zukatansu. Don haka ne ma ake yawan yin amfani da matasan Arewa ta fuskoki da dama don cika burin da wasu gurɓatattun mutane dalilin kasancewarsu karnukan Yahudawa suke son cimmawa.
Ana amfani da matasanmu na Arewa wajen bangar siyasa, wanda hakan ke jefa su cikin mummunar hanyar ta’ammuli da miyagun ƙwayoyi, da ayyukan Daba, da ƙwace da makami da sauransu. Waɗanda su ke saka matasa a wannan hanya kuma su ne ‘yan siyasa, wanda idan suna ɗaukar matasan a wancan aiki ba za ka taɓa ganin ‘ya’yansu a ciki ba, koda ‘ya’yan suna shan miyagun ƙwayoyi. Za ka samu cewa sun killace iyalansu a waje mai kyau, ga abinci da abin sha mai kyau, ga kuɗaɗe a asusun ajiyarsu na Banki, suna karatu a makarantun kuɗi na gida ko ƙasashen Turai ma su tsada. Duk wani ɗan siyasa ɗan Arewa, babu wanda bai san abin da a ke shiryawa yankinsa na Arewa ba na makirci da yunƙurin rusata ba. Amma babu wanda su ke zalunta sai mutanen yankin, yankin da shi ne babban ginshiƙin gina Nijeriya.
‘Yan siyasar kudu ba sa samun cikakkiyar dama da goyon bayan al’ummarsu a kan jagorantar al’umma, har sai sun zauna da al’ummar da za su wakilta a kowanne matsayi sun yi jarjejeniyar abin da za su yi na ci gaba idan sun hau madafun iko. Babu wani ɗan siyasar da zai samu mara bayan al’umma a yankin kudancin ƙasar nan, sai al’umma sun gabatar masa da buƙatunsu ya amince tare da ɗaukar alƙawarin zai yi musu duk abin da suke so, sannan ya sa hannu a takardar yarjejeniya suma kuma su sa hannu. To amma mu a yankin Arewa ya muke? Duk wani ɗan siyasar da zai fito neman ƙuri’ar al’umma ba ya cika alƙawurran da yake ɗauka idan ya ci zaɓe, idan ya ɗare kan matsayin, to shi kenan sai al’ummar da suka zaɓe shi ya kai matsayin da yaje su neme shi su rasa, amma hakan ba ya hana idan ya ƙare shekarun mulkinsa ba tare da ya yi musu aikin komai ba, idan ya dawo karo na biyu su sake zaɓarsa, saboda ɗan abin da zai zo ya lasa musu.
Magana a kan rusa Arewacin Nijeriya da nake so na sake yi a wannan karon, ina so in sake haska wa mutanen Arewa hoton abubuwan da ya kamata su sani ne, sannan kuma su san abin da ke gabansu, da abinda zai same mu a Arewa idan mun ci gaba da zama muka rungume hannaye muna cewa “BAKIN DA ALLAH YA TSAGA, BA YA HANA SHI ABINCI”. To wallahi tallahi ina so in shaida mana cewa, yana daga cikin mummunan shirin da aka shiryawa yankin Arewa haifar mana da gaba a tsakaninmu da sunan Dimokraɗiyya, da ƙirƙirar mana talauci da yunwa, bayan kuma Allah Ya azurta mu da ƙasar noma.
Tsakani da Allah matasanmu na Arewa lokaci yayi da ya kamata ku san ciwon kanku, kuyi kishin ƙasarku. Makircin da aka ƙullo wa yankin Arewa ba ƙarami ba ne, kuna ji kuna gani da idanunku na abubuwan da ake yi mana a Arewa. Jihar Borno, Taraba, Adamawa, Yobe, Bauchi da Platoue duk a Arewa suke, a waɗannan jihohin an kashe biliyoyin al’umma, baya ga rusa garuruwan wasu da raba su da dabbobinsu. Idan muka dawo jihar Katsina, Kaduna, Zamfara, Sokoto, Kebbi da Niger kuwa, har yanzu ana kashe rayukan dubban al’umma mazauna karkara da ba su aikata laifin komai ba, ana garkuwa dasu a biys kuɗin fansa, ana ƙona masu gari da amfanin gona, ana yanka musu haraji su biya, kuma duk da wannan ta’addanci da ‘yan bindiga suke yi wa waɗannan al’ummomi a waɗancan yankuna, kuma a haka suke biyan harajin kayan amfanin gonar da suke nomawa idan sun kai kasuwa, su biya harajin hanya, idan sun sayo kaya daga wani waje za su dawo gida jami’an tsaro su karɓi kuɗi a hannunsu.
Duk wani abu da muke tunƙaho da shi a yankin Arewa bai kai darajar noma da kiwo ba, amma muna ji muna gani yunwa ta addabe mu, mun shiga ƙuncin rayuwa a sanadiyyar taɓarɓarewar tsaro a Arewa. Idan ka ce zaka fito ka faɗa wa Gwamnati gaskiya a kan rashin kulawa na ɗaukar matakin da ya dace sai a ce ka zama ɗan adawar gwamnati, sai a fara yi maka barazana da rayuwarka, idan kayi karanka ya kai tsaiko sai a turo maka wasu kuɗaɗe don kayi gum da bakinka, idan ka ƙi amincewa don kishin ƙasa, sai a nemi wani sharri a ƙaƙaba maka. Kamar yadda muka ga an yi a kan shugaban ƙungiyar ƙwadago Joe Ajure da wasu.
Ko a lokacin mulkin tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, mun ga yadda gwamnatinsa ta rika kama waɗanda suke suka tare da faɗa wa gwamnati gaskiya, idan kuma kai ɗan jam’iyyar adawa ne a siyasance ka ke sukar gwamnatin Buhari, to da zarar ka shiga jam’iyyarsu dake mulki shi kenan ruwa ta sha. Mun ga yadda tsohuwar gwamnatin Buhari ta riƙa yi wa ‘yan adawa bi-ta-da-ƙulli don kawai suna sukar tsauraran matakan da gwamnatin Buhari da ta shuɗe ke ɗauka, wanda su ne ummul’aba’isin jefa al’ummar Nijeriya halin ƙuncin da muke gani a yau.
To ita ma wannan gwamnatin mai ci yanzu ta Bola Tinubu, haka ta ke yi. Duk wanda yake sukarta a kan tsauraran matakan da take ɗauka shi kenan sai ya zama abin farautarta. Mun ga yadda aka kama wasu matasan ƙasar nan da sunan wai sun tunzura mutane, ko sun jagoranci mutane wajen zanga-zangar da aka yi a ranar 10 ga watan August da ya gabata, haka nan mun ga yadda gwamnatin Tinubu ta fito ta ce, babu albashi ga Likitocin da suke aikin jinya a Kaduna, don kawai sun yi yajin aiki a kan garkuwa da abokiyar aikinsu a Kaduna, wacce har yanzu ba a sako ta ba. Haka nan mun ga yadda jami’an DSS suke bin mutanen da suke adawa da wannan gwamnatin a kan matakan da take ɗauka har filayen jiragen sama tana kamawa.
Shin yanzu shi kenan idan an zalunce ka a matsayin ɗan Nijeriya ba za ka koka ba? Shin haka zamu zauna ana dukanmu ana hana mu kuka? Dole matasan ƙasar nan mu tashi tsaye mu kawo sauyi, ko muna so ko ba ma so. Wallahi zama muyi shiru ba namu ba ne, raye-raye da ɗora waƙoƙi a Tiktok da duk wata kafar internet ba namu ba ne. Wajibi ne mu tashi tsaye muyi yaƙi da zalunci domin ƙwato martabar kanmu da ta yankinmu na Arewa.
Abin takaici ne a gare mu a ce mun tsaya muna shirme da shashanci a kafafen sada zumunta na (social media), a maimakon mu riƙa yin abubuwan da suka dace, nuna damuwarmu a kan halin da mune ciki, nuna adawa da zaluncin shugabanninmu. Dole ne muyi amfani da kafar sadarwar zamani wajen yaƙi da mulkin zalunci, muyi rubuce-rubuce, mu nuna hotuna da bidiyoyin duk wata badaƙalar da ake mana.
Wannan wajibi ne, don kawai manyan Arewa sun karɓi kuɗi sun sayar mana da yanki, sun sayar mana da ‘yanci, sun karɓi kwangilar kashe mu, da rusa mu, to ba zai yiwu mu zuba ido hakan taci gaba da faruwa ba. Nijeriya ƙasarmu ce ta haihuwa, yankin Arewa yankinmu ne da zamu yi tunƙaho da shi. Amma haka kawai mun zuba ido ana lalata mana yanki, ana haɗa mu faɗa da junanmu, ana kwashe mana arzikinmu, ana kashe mana mutane, ana danne mana ‘yanci.
Daga NAFI’U SALISU.
Marubuci/manazarci. [email protected]. [email protected]. 08038981211-09056507471.
