‘Yan banga sun yi nasarar kashe makusancin Turji, Kachalla Sani Black

Spread the love

Ɗan bindigar da ya shahara da sunan Kachalla Sani Black, ya mutu a hannun ‘yan banga.

‘Yan bangar da suka yi wannan aikin sun kuma bindigu biyu AK-47, kuɗi da ba a bayyana adadin su ba da kuma bindigar PKT.

PRNigeria ta kuma tattara cewa ‘yan bangar gida suka kashe Kachalla da ‘ya’yansa biyu a wani kwantan ɓauna a Magama Mai Rake, a karamar hukumar Maru.

Kachalla Sani Black, yana da alaƙa da Bello Turji a ta’addancida ya ke aikatawa. Kuma ya kasance shugaban ‘yan bindiga da ya shahara a Chabi, yankin Ɗan Sadau na karamar hukumar Maru.

PRNigeria ta rawaito cewa Sani- Black ɗan ta’adda da ya addabi al’ummomi da masu tafiya a Arewacin Zamfara, ya kai hare-hare a Kaduna, Neja, da Kebbi.

A shekarar 2021, ‘yan sanda sun cafke ɗaya daga cikin ‘yaransa, Sani Mati Mai Yanmata wanda ya ƙware wajen sace sacen mata, fyaɗe, ciki har da matan aure da masu juna biyu a ƙananan hukumomin Shinkafi, Zurmi, da Birnin Magaji na Jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan Zamfara na lokacin, CP Ayuba Elkanah, ya bayyana cewa an kama ɗan ta’addan ne yayin da yake ƙoƙarin tare wata hanya domin yin fashin da suka saba.

By ukarofi