An sace babur ɗin ɗan jarida a gidan gwamnatin Bauchi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Alhamis da ta gabata ne aka sace babur ɗin wani wakilin gidan telebijin na AIT mai suna Damina Yusuf a gidan gwamnatin jihar Bauchi, bayan gayyatar sa zuwa wani taro da aka yi.

Ɗan jaridar, wanda ke zama a Bauchi, an gayyace shi ne don ɗaukar rahoton wani shiri na “Renewed Hope Agenda” wanda matar shugaban ƙasa, Misis Remi Tinubu da na gwamnan jihar Bauchi, Hajiya A’isha Bala Mohammed suka shirya don inganta mata a jihar.

Jaridar ‘WikkiTimes’ ta ruwaito cewa, ɗan jaridar ya ce, “an baza jami’an tsaro sosai a lokacin da na ke ƙoƙarin shiga, inda ƴan sanda suka tare ni kuma suka hana ni shiga. Ƴan sandan sun umarce ni na ajiye babur ɗina a waje inda akwai wasu babura kusan 20.”

Ya ce, bayan ya kammala aikinsa ne sai ya fito don ɗaukar babur ɗin inda ya tarar babu shi a wajen da ya ajiye.

A lokacin da ya sanar da ƴan sandan gidan gwamnatin, sai suka ce masa za su duba ɗauɗaukar kamarorin tsaron gidan don gano wanda ya ɗauke inda suka karɓi lambar wayarsa tare da ba shi ta wani Sufeto Buba.

Daga nan ne, sai ya sanar da Sakatariyar labarai, Murjanatu abin da ya faru inda ta nuna damuwa tare da sanar da matar gwamnan.

By Babaji