Dalilin da ya sa Turji ke cikin firgici – Hafsan Sojoji

Spread the love

Babban Hafsan Tsaron ƙasa, CDS, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa, jagoran ‘yan bindiga da ake nema, Bello Turji, yana cikin yanayin firgici sakamakon sabon farmakin sojoji kan ‘yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma.

Musa ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a gefe na taron farko na NAN na ƙasa da ƙasa da aka gudanar a ranar Alhamis a Abuja.

Musa ya bayyana cewa kashe Halilu Buzu da sauran manyan kwamandojin ‘yan bindigan ya jefa firgici a sansanin Turji da mabiyansa, yana mai cewa matakan da yake ɗauka a yanzu suna nuna alamun tsoro da razana.

“Yanzu ya san cewa ba shi ne ke da iko ba. Ya san cewa lokaci ne kawai ya rage masa saboda Halilu Buzu da aka kashe shi ne ubangidansa.
“Saboda haka, yanzu da ya san cewa kwamandan nasa ya mutu, ya san cewa shi ne na gaba, don haka duk abin da yake yi a yanzu shirme ne kawai,” inji shi.

Janar Musa ya cigaba da bayyana cewa shugaban ‘yan bindigan ya ketare layi don haka dole a hukunta shi.

By ukarofi