Tinubu ya miƙa wuya ga buƙatar Majalisar Wakilai ta bai wa kakakinta lambar GCON

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da buƙatar Majalisar Wakilai na a bai wa kakakinta, Tajuddeen Abbas matsayin GCON (Grand Commander of the Order of the Niger).

Hakan na zuwa ne bayan nuna rashin amincewa da mambobin majalisar suka yi na ayyana kakakin da mataimakin shugaban Majalisar Dattijai a matsayin CFR, wato ‘Commander of the Federal Republic’ da Shugaba Tinubu ya yi a jawabinsa na ranar zagayowar ƴancin kai.

Hakan ya haifar da muhawara a zauren Majalisar, a ranar Laraba ne mambobin suka nuna cewa kakakin nasu ya cancanci lambar girma sama da wannan.

Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan yaɗa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga ya ce, Tinubu ya miƙa wuya ga buƙatar Majalisar tare da sauya matsayarsa la’akari da yadda dokar ƙasa ta nuna.

By Babaji