
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya umarci Hukumar Kiyaye haɗɗura ta Ƙasa da ta aiwatar da sabbin matakan kariya a kan titinan dake faɗin Nijeriya don rage yawan afkuwar haɗurra.
Shettima ya bayar da umarnin ne a yayin da ya karɓi baƙoncin shugaban hukumar, Marshal Shehu Muhammad da wasu ƙusoshin hukumar a Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
A yayin baƙoncin, Shettima ya ƙaddamar da majalisar bayar da shawara kan dabarun kiyaye afkuwar haɗɗura wadda aka ɗora wa alhakin rage afkuwar haɗɗura kafin shekarar 2030.
Hakazalika, Shettima wanda shi ke jan ragamar Majalisar ya ƙara nuna muhimmanci amfani da fasahar zamani wajen hana aukuwar haɗura a tituna.
“Muna buƙatar jajircewwa da dabaru wajen tunkarar ƙalubalen haɗura a titunan mu. Hakan zai sa mu yi gogayya da manyan titunan da ke ƙasashen duniya, kamar ƙasar Birtaniya da birnin Dubai”, inji Shettima.
Sabbin mambobin kwamitin sun haɗa da; gwamnoni, ministoci da kuma shugabannin ƙananan hukumomi na ƙasa.
