‘
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gumurzun faɗa a ɓangarorin ‘yan bindiga a garin Ɗan Ali a ƙaramar hukumar Ɗanmusa ya sanya dole jama’ar Musulmi da suka je sallar Juma’a a garin suka ranta a na kare kafin gudanar da sallar Juma’a.
Wani mazaunin garin da bai so a faɗi sunan shi yace wannan faɗa ne da aka daɗe ana gwabzawa tsakanin Buzare da Nure waɗanda da abokai ne amma yanzu suka zama abokan gaba.
Ya ce kowanan su yana jagorantar gungun yan ta’adda a yankin ƙaramar hukumar Ɗanmusa da suka maida sansaninsu.
Ya cigaba da bayyana cewa shi Buzare na riƙe da ƙauyukan Ɗan Ali da Mara Zamfara da Mara Katsina, shi kuma Nure yana riƙe da Yan tumaki da Maidamu da garin Ɗanmusa.
Mazaunin garin ya ce kusan mako guda kenan suke ta gwabza ƙazamin faɗa da ya kawo sanadiyyar mutuwar yan ta’addan fiye da 20.
Sai ya ce daga baya ranar Juma’ar jami’an tsaro na al’umma na ‘community watch’ sun shigo garin suma sai da su ka nemi ƙarin jami’an su sannan suka fatattaki ‘yan bindigan.
Ya kuma bayyana cewa a yanzu haka ‘yan ta’addan sun hana manoma na garin Ɗan Ali da ƙauyukan Gwarjo, Dangane,Tashar Biri da Tashar kaɗanya zuwa girbe amfanin gonarsu.
Wakilinmu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun ‘yan sanda a Katsina ASP Abubakar Sadiq Aliyu amma bai ɗauki waya ba sai dai ya aiko saƙo a tura masa tambayar, an aika masa har ya zuwa yanzu bai bada amsa ba.
