
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Hukumar bada ilimi a matakin farko, SUBEB ta fara horar da yara ƴan makarantun firamare yadda ake kiwon kaji a Jihar Katsina.
Shugaban hukumar, Dakta Kabir Magaji ya sanar da haka a wata hira da manema labarai a ofisoshinsa inda ya ce hukumar ta ware makarantu 120 domin gudanar da shirin.
Daktan ya kuma ce, hukumar ta kashe Naira miliyan 48 wajen sayan kajin kiwo da abincinsu tare da biyan alawus na malaman da ke horar da ɗaliban.
Ya bayyana cewa, hukumar ta ƙirƙiro da shirin ne domin taimaka wa ɗaliban su zama masu dogaro da kai bayan sun kammala karatunsu na firamare.
Shugaban hukumar ya kuma yi cikakken bayanin irin ci-gaban da hukumar ta samu ƙarƙashin gwamnatin Dikko Raɗɗa.
Ya sanar da cewa hukumar ta samu kuɗi da adadinsa ya kai Naira miliyan dubu sha-biyar a matsayin kuɗin haɗin-gwiwa daga gwamnatin Katsina da hukumar bada ilimi ta ƙasa a cikin watanni 14.
Dakta Kabir ya bayyana cewa hukumar ta gyara tare da gina wasu sabbin makarantu a faɗin jihar da kuma ɗaukar malamai fiye da 5000.
Sauran aikace-aikacen da hukumar ta gudanar sun haɗa da; samar da tebura da kujeru na karatu da kuma ɗaukar nauyin horar da malamai akai-akai.
