
Daga BELLO A. BABAJI
Babban lauyan Nijeriya (SAN), Femi Falana ya musanta cewa ya san ɗan basaja, Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky.
Falana ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na ‘channels’ inda ya ce babu wata alaƙa da ta taɓa shiga tsakanin sa da Bobrisky.
Amma ya ce, Bobrisky ya tattauna da ɗansa, Folarin Falana da aka fi sani da Falz.
Wani mawallafi mai suna Martins Otse da ake kira da VeryDarkMan ya sanya ɗaukar murya da ke zargin cewa, babban lauyan ya karɓi cin-hancin Naira miliyan 10 daga Bobrisky don neman masa yafiya daga fadar shugaban ƙasa.
Saidai, VeryDarkMan ya nemi afuwa daga Femi Falana a ranar Litinin, a lokacin da ya hallara a gaban kwamitin laifukan da suka shafi kuɗi da gyaran cibiyoyi na Majalisar Wakilan Nijeriya.
Falana ya ce, ya nema wa mutane da ake tuhuma da laifuka da adadinsu ya kai 280 afuwa ba tare da karɓar ko sisin kwabo ba.
Falana ya ce, “Bobrisky bai taɓa magana da ni ba, ban taɓa haɗuwa da shi ba. Ban san shi ba. An ce ya yi magana da ɗana Folarin.”
Babban lauyan ya kuma bayyana wayar da Folarin ya yi da ɗan basajar, inda ya ce ya kira ɗan nasa a ranar 4 ga watan Mayu ya na neman ba shi cin-hancin Naira miliyan 3 don a sanya shi a waje na musamman a gidan yari. Saboda haka ne, ɗan ya ƙi amincewa tare da gargaɗin Bobrisky kan cewa kar ya sake kiransa da sunan zai bada cin-hanci don a bai wa jami’an gidan yarin.
