
Daga BELLO A BABAJI
Wasu mutane da ake zargi sun sanya bom a sakatariyar jam’iyyar APC da ke Fatakwal a Ribas yayin da ake gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar a yau Asabar.
Wata ɗaukar bidiyo ta nuna yadda abin fashewar ya tarwatse a ƙofofin shiga sakatariyar.
Cikin wani gajeren saƙo da shugaban jam’iyyar na riƙon ƙwarya a jihar, Cif Tony Okocha ya aika wa manema labarai ya zargi magoya bayan Gwamnan jihar Siminalayi Fubara na jam’iyyar PDP da ɗanyen aikin.
Ana gudanar da zaɓen ne cikin lumana a sassa daban-daban na jihar duk da cewa rundunar ƴan sanda ta tsame hannunta acikin harkokin zaɓen sakamakon umarnin kotu.
Sannan, ana gudanar da zaɓen ne a gundumomi 319 da mazaɓu 6,366 a ƙananan hukumomi 23 na jihar.
Haka nan, sha takwas daga cikin halastattun jam’iyyu 19 a Nijeriya ke fafatawa a zaɓen.
