Rashin Tsaro: Gwamnatin Sakkwato ta fara gina sansanin sojoji a Illela

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ce ta na gina sansanin sojoji a garin Illela a ƙoƙarinta na taimaka wa jami’an tsaro wajen kawo ƙarshen ta’addanci a jihar.

Mai bai wa gwamnan shawara ka harkar tattali, Dakta Bashir Achida ya bayyana hakan wa ‘News Agency Nigeria’ a ranar Juma’a inda ya ce yunƙurin wani mataki ne na samar da zaman lafiya a jihar da yankin Arewa-maso-Yammacin Nijeriya baki ɗaya.

Ya ce, bayan kammala aikin sansanin ne, gwamnatin jihar za ta miƙa wa ta tarayya kamar yadda doka ta amince.

Ya kuma ce, ci-gaban ya na da muhimmanci wajen ganin an kare rayuka da dukiyoyin al’umma musamman kan yadda su ke taka rawar gani ga noma a jihar da ma ci-gaban tattali a mataki na ƙasa.

Haka nan Dakta Achida ya ce, kasancewar jihar ta na da ƙasar noma wanda mafi yawancinta na da iyaka da wasu ƙasashe, hakan ya bai wa ƴan ta’adda damar cin karensu ba babbaka.

Kazalika, ya ce gwamnati ta samar da motoci 140 ga hukumomin tsaro a jihar don yaƙar ta’addanci da ƴan bindiga a yankunan al’umma da kuma wuraren noma.

By Babaji